Tsadar Siminti: Kamfanoni Sun Yi Biris da Kiran Majalisa Kan Sauke Farashi
- Mayan kamfanonin siminti a Najeriya sun yi biris da kiran da majlisar wakilai tayi masu kan gurfana a gabanta a yau Litinin
- Dama dai majalisar ta gayyace su ne makonni da suka wuce kan su gurfana a gabanta domin yin bayani a kan tashin farashi
- Sai dai shugaban kwamitin binciken, Jonathan Gaza Gefwi ya bayyana dalilan da suka hana kamfanonin a amsa gayyatarsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Kwamitin da ke bincike kan karin kudin siminti ya bayyana halin da ake ciki kan zama da majalisar wakilai za ta yi da manyan kamfanonin siminti a Najeriya.
Masu hada siminti da 'yan majalisa
A yau Litinin ne majalisar ta gayyaci manyan kamfanonin domin su gurfana a gabanta kan shawo tsadar siminti a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma sai dai rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa kamfanonin ba su gurfana a gaban majalisar ba kamar yadda suka bijire a baya.
Meya hana kamfanonin zuwa majalisa?
Shugaban kwamitin binciken tashin farashin siminti da majalisar ta kafa, Jonathan Gaza Gefwi ya ce kamfanonin suna fakewa da umurnin kotu wurin kin amsa gayyatarsu.
'Dan majalisar ya bayyana haka ne a zamansu na yau yayin da suke tsammanin gurfanar kamfanonin a gabansu.
Majalisa ta gargadi kamfanonin siminti
Shugaban kwamitin binciken ya ce wannan ba shi ne karon farko da kamfanonin ke bijirewa gayyatar majalisar ba.
Saboda haka ya ja kunnensu da su daina yin dabaru wajen kaucewa binciken da majalisar ke gudanarwa, rahoton Vanguard
Umurnin da kotu ta ba kamfanonin siminti
Har ila yau shugaban kwamitin ya ce kamfanonin sun gabatar da wata shaida ce wacce ta ke nuna rashin amincewa da cigaba da bincikensu daga babbar kotun tarayya.
Amma sai dai shugaban ya ce hukuncin da ke cikin takardar wani tsohon zance ne wanda bai shafi binciken da suke yi a halin yanzu ba.
Majalisa ta gayyaci kamfanonin siminti
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta gayyaci Dangote, BUA da sauran kamfanonin siminti a Najeriya domin tattauna wa kan tsadar siminti a kasar nan.
Gayyatar ta ya biyo bayan kudirin da Hon. Gaza Jonathan Gbefwi, da Hon. Ademorin Kuye suka gabatar yayin wani zaman majalisar a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng