Ebrahim Raisi: Muhimman Abubuwa 5 da Baku Sani Ba Kan Shugaban Ƙasar Iran da Ya Rasu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A ranar Lahadi, 19 ga watan Mayu, shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi, ya rasu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar angulu.
Jami'an ceto a ranar Litinin sun gano jirgin da ke dauke da shugaban kasar Iran, kuma ministan harkokin wajen kasar, Hossein Amirabdollahian, da wasu manyan jami'ai.
Kamar yadda Tribune Online ta ruwaito, jirgin helikwaftan da shugaban ƙasar ke ciki ya faɗo ne a tsaunukan da ke Arewa maso Yammacin ƙasar Iran.
Legit Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa bakwai (7) da wataƙila ba ku sani ba game da Marigayi Shugaban Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Haihuwa
An haifi marigayi shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi a ranar 14 ga watan Disamba, 1960 a garin Mashhad, wata cibiyar ƙungiyar Shi'ah mai limamai 12.
2. Ilimi
Raisi ya fara karatu a makarantar hauza ta Qom yana ɗan shekara 15 da haihuwa bayan ya kammala karatun firamare a makarantar Javadiyeh.
A shekarar 1975, ya tafi makarantar Ayatollah Boroujerdi don ci gaba da karatunsa da ya fara a makarantar hauza ta Qum.
3. Ya riƙe kujerar Antoni Janar a Iran
Raisi ya zauna a kujerar Antoni Janar na ƙasar Iran a 2014, inda ya shafe tsawon shekaru biyu gabannin Khamenei ya naɗa shi domin ya jagoranci Astan Quds Razavi.
A wani lokaci an raɗawa marigayi shugaban Iran sunan, ''Mahaucin Teheran,' saboda sa hannun da ya yi a kisan da aka yi wa fursunonin siyasa a 1988.
Ya zama shugaban Astan Quds Razavi a ranar 7 ga Maris 2016 bayan mutuwar magabacinsa Abbas Vaez-Tabasi, mukamin da ya shafe tsawon shekaru uku a kai.
4. Yadda ya zama shugaban kasar Iran
Ebrahim Raisi ya samu nasarar zama shugaban ƙasar Iran a zaɓen 2021 duk da ƙarancin fitowar masu ƙaɗa kuri'a.
Masu neman sauyi a ƙasar sun nuna rashin gamsuwar da takarar Raisi a zaɓen yayin da da yawa daga cikin sauran ƴan takara suka nuna adawa da shi.
5. Iyalin marigayi Ebrahim Raisi
Marigayi Raisi yana da mata ɗaya, Jamileh Alamolhoda, ɗiyar babban limamin masallacin Jumu'a na Mashhad, Ahmad Alamolhoda.
Allah ya albarkaci ma'auratan da haihuwar ƴaƴa guda biyu, kuma suna da jikoki da dama.
Afonja: Tsohon ministan kwadago ya rasu
A wani rahoton kuma tsohon ministan kwadago kuma tsohon shugaban First Bank, Prince Ajibola Afonja ya riga mu gidan gaskiya a asibitin UCH.
Rahotannin da suka fito ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, sun nuna cewa Afonja, wanda ake kira IDS ya mutu ne ranar Lahadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng