Wanene Mohammad Mokhber, Shugaban Rikon Kwaryan Kasar Iran? Abin da Muka Sani
Kasar Iran - A yau Litinin, 20 ga watan Mayu, aka tabbatar da mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a jiya Lahadi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Mun ruwaito yadda hatsarin ya faru da kuma abubuwan da suka biyo baya har zuwa kan batun rantsar da shugaban riko na kasar Iran, Mohammad Mokhber.
Kamfanin labaran Iran, ya ruwaito cewa kakakin majalisar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Hadi Tahan Nazif ya sanar da cewa Mokhber zai karbi ragamar shugabancin rikon kwarya.
Ga wasu muhimman bayanai game da Mohammad Mokhber mai shekaru 68, mataimakin shugaban kasar Iran na farko wanda ya zama shugaban rikon kwarya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mokhber ya shiga majalisar mutum uku
A matsayinsa na shugaban rikon kwarya, Mohammad Mokhber na cikin wata majalisa mai mutum uku, tare da kakakin majalisar dokoki da kuma shugaban bangaren shari'a.
Reuters ta ruwaito cewa 'yan majalisar ne za su shirya sabon zaben shugaban kasa cikin kwanaki 50 da rasuwar shugaban.
Tasirin Mokhber zuwa zama mataimakin Raisi
Kamar marigayi Raisi, ana kallon Mokhber, wanda aka haifa a ranar 1 ga Satumba, 1955, a matsayin na kusa da Jagora Ali Khamenei, wanda ke fada a ji a dukkanin al'amuran kasar Iran.
Mokhber ya zama mataimakin shugaban kasar Iran na farko a shekarar 2021 lokacin da aka zabi Raisi a matsayin shugaban kasa.
Zuwan Mokhber Moscow kan makamai
Mokhber na cikin tawagar jami'an Iran da suka ziyarci birnin Moscow a watan Oktoba inda suka amince da samar da makamai masu linzami da kuma karin jirage marasa matuka ga sojojin Rasha
Tawagar ta kuma hada da wasu manyan jami'ai biyu na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da kuma wani jami'in kwamitin kolin tsaron kasar, in ji rahoton Reuters.
Mokhber na jagorantar hukumar Setad
A baya, Mokhber ya kasance shugaban Setad, hukumar kula da asusun saka hannun jari da ke da alaƙa da shugaban kasar (marigayi).
EU ta kakabawa Mokhber takunkumi
A cikin 2010, Tarayyar Turai ta saka Mokhber a cikin jerin mutane da ƙungiyoyin da ta sanya wa takunkumi kan zargin sa hannu a "ayyukan makami mai linzami na nukiliya ko ballistic".
Bayan shekaru biyu, kungiyar EU ta cire shi daga jerin masu wannan takunkumi.
Iran: Mutuwar Shugaba Raisi a hatsarin jirgi
Tun da fari, mun ruwaito cewa abubuwa da dama sun faru a kasar Iran tun bayan hatsarin jirgin sama da ya yi silar mutuwar shugaban kasar, Ebrahim Raisi.
Mun zayyano wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da hatsarin jirgin, abin da kasashen duniya ke cewa da kuma matakan da aka dauka a yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng