Ministar Tinubu da Uba Sani Za Su Halarci Muhimmin Taro a Birnin Landan
- Doris Nkiruka Uzoka-Anite, ministar masana'antu, ciniki da zuba jari za ta halarci taron zuba jari na ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje a birnin Landan
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da wata tawagar shugaban ƙasa na daga cikin mutanen da za su halarci taron a ranar 24 ga watan Mayu
- Uba Sani zai kasance babban mai jawabi a wajen taron wanda zai samu halartar shugabannin ƴan kasuwa na ƙasashen waje da ƙasashen Afirika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministar masana’antu, ciniki da zuba jari, Doris Nkiruka Uzoka-Anite, za ta kasance babbar baƙuwa ta musamman a wurin taron zuba jari na ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NDDIS).
Masu shirya taron da za a gudanar a ranar, 24 ga watan Mayu a birnin Landan suka tabbatar da hakan.
Me gwamna Uba Sani zai yi a taron?
Taron mai taken 'Invest Nigeria, Invest Africa' zai samu halartar gwamnan jihar Kaduna Uba Sani a matsayin babban mai jawabi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran mahalarta taron sun haɗa da babbar mai ba shugaban ƙasa shawara kan samar da ayyukan yi da ƙananan sana'o'i, Temitola Emitola Adekunle Johnson.
A tawagar akwai shugabar hukumar ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Hon. Abike Dabiri Erewa.
A cewar sanarwar da daraktan yaɗa labarai ta ƙungiyar, Lady Doyin Ola ta fitar, taron zai samu halartar shugabannin ƴan kasuwa na ƙasashen waje da ƙasashen Afirka, Birtaniya, da ƙasashe rainon Ingila da sauran masu zuba hannun jari.
Za a ba da bashi kyauta
Tun da farko wanda ya kafa NDDIS, Prince Bimbo Roberts Folayan, ya ce sun samu ci gaba a tattaunawar da suke yi da waɗanda za su ɗauki nauyin shirin ta hanyar ba da kaso 100% na bashin da ba za a biya ba, cewar rahoton Independent.
"Na yi matukar farin ciki sosai game da taron na bana domin a karon farko, za mu shiga cikin aikin tantance ayyukan sannan kuma za mu taimaka wajen tura ayyukan da suka cimma muradun SDG domin samun tallafi.
"Wannan dai shi ne karon farko da aka ba mu wannan dama tun lokacin da muka fara jawo ayyuka a Najeriya da Afirika."
- Prince Bimbo Roberts Folayan
Doris Anite ta gana da Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da ministar masana'antu, ciniki da zuba jari, Doris Anite a birnin Kano.
Gwamnan ya gana da ministar ne domin nemo hanyoyin bunƙasa kasuwanci a jihar wacce ta kasance cibiyar kasuwanci musamman a Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng