Sojoji Sun Ceto Mutum 386 Da ’Yan Boko Haram Suka Sace Tsawon Shekaru 10
- Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto wasu mutanen da ‘yan ta’adda suka sace tsawon shekaru 10 zuwa yanzu
- An bayyana sabon aikin da sojojin suka fara domin tabbatar da sun kakkabe dajin Sambisa daga masu aikata ta’addanci
- Jihohin Arewa maso Gabas na fuskantar matsalolin da suka shafi tsaro, musamman aikin ta’addancin Boko Haram da ISWAP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Borno - Akalla mutane 386 ne da akasari mata da kananan yara sojoji suka ceto a dajin Sambisa shekaru goma bayan sace su.
Mukaddashin GOC na shiyya ta 7 a rundunar soji, AGL Haruna ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a dajin Sambisa a karamar hukumar Konduga bayan tarbar sojojin da suka gudanar da aikin na kwanaki 10.
A cewarsa, farmakin da aka yi wa lakabi da “Operation Desert Sanity 111” an fara shi ne a aikin share dajin Sambisa daga dukkan nau’ikan ‘yan ta’adda a yankin, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aikin da sojoji ke yi a yanzu
Da yake jawabi, y ace:
“Kokarin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ‘yan ta’adda a Sambisa tare da baiwa masu son tuba damar mika wuya.
“Da wannan aikin, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su mika wuya kamar yadda suka fara.
“Mun kuma ceto wasu fararen hula; ya zuwa jiya mun ceto 386 kuma na tabbata adadin zai karu zuwa yau.”
An yabawa sojoji bisa aikin ceto ‘yan kasa
A yayin da yake yiwa sojojin bayani kan sakon babban hafsan sojin kasar, ya yaba da kwazon da suka nuna a lokacin aikin, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da aikinsu yadda ya dace.
Wasu daga cikin wadanda aka ceto da suka yi magana da manema labarai sun ce shekaru 10 da suka gabata aka yi garkuwa da su, Ripple Nigeria ta ruwaito.
An kame barayin mota a Enugu
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Enugu a Kudu maso Gabashin Najeriya ta ce ta kama wasu yara maza biyu da ake zargi da laifin fashi da makami a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a 17 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng