An Samu Yamutsi Bayan Bata Gari Sun Afkawa Sojoji a Abuja

An Samu Yamutsi Bayan Bata Gari Sun Afkawa Sojoji a Abuja

  • An samu yamutsi a kasuwar Banex da ke Wuse a birnin tarayya Abuja tsakanin wasu bata gari da jami'an sojin Najeriya
  • Yamutsin ya faru ne a yammacin yau Asabar, 18 ga watan Mayu biyo bayan sabani da aka samu tsakanin bangarorin biyu
  • Duk da cewa jami'an tsaro ba su ce komai game da lamarin ba, jami'an yan sanda sun je kasuwar domin daukar mataki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

An samu yamutsi a kasuwar Banex da ke birnin tarayya Abuja bayan wasu bata gari sun afkawa sojojin Najeriya.

Banex market
An watse a kasuwar Banex bayan wasu bata gari sun yi fada da sojoji. Hoto: Obi Kekong
Asali: Facebook

Lamarin ya faru ne a yammacin yau Asabar, 18 ga watan Mayu a yankin Wuse da ke birnin Abuja.

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da dattijo mai shekaru 50 ya mutu yana tsaka da kallon ƙwallo

Duk da cewa zuwa yanzu ba samu cikakken bayani kan abin da ya jawo yamutsin ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an samu sabani ne tsakanin sojoji da wasu mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabi daga bakin wani dan kasuwa

Wani mai shago a kasuwar ya tabbatar da cewa fada ya kaure tsakanin sojojin da wasu mutane ne bayan an sun samu sabani. Ga abin da yake cewa:

"Duk da cewa bana kasuwar a lokacin da abin ya faru, amma na kira yaron shago na a wayar tarho kuma ya tabbatar min da cewa an samu sabani ne tsakanin sojoji da wani mutum."

Abin da Legit ta tattaro a wani bidiyo

A wani faifayin bidiyo da ya nuna yadda rikicin ya kaure an hasko sojoji sanye da kaya suna jayayya da wasu mutane.

Mutanen sai suka raba kansu gida uku suka fara kai wa sojojin hari mai muni, daga nan ne sai kasuwar ta rikice.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Daga baya sai mutane suka fara rige-rige wajen rufe shaguna suna guduwa daga cikin kasuwar cikin gaggawa.

Jami'an tsaro ba su ce komai ba

Yunkurin ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ya ci tura ta yadda ba ta amsa wayar tarho ba.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an yan sanda sun isa kasuwar cikin gaggawa domin zuba wa wutar ruwa, cewar jaridar Punch.

Jami'an tsaro sun yi rikici a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rikici ya ɓarke tsakanin wasu jami'an DSS da ma'aikata a zauren majalisar tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne lokacin da jami'an DSS suka hana wasu manyan ma'aikata wucewa har suka fara hayaniya, wanda ya ja hankalin sauran ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng