Naira Ta Sake Tashi a Karo na 2 a Cikin Mako 1, Ta Karu da Kusan N100
- An sake shiga murna yayin da Naira ta sake tashi tare da yin nasara kan dala a kasuwannin gwamnati da na bayan fage
- Darajar Naira ta sake farfaɗowa da kusan karin N100 a ranar Juma'a 17 ga watan Mayu idan aka kwatanta da ranar Alhamis 17 ga watan Mayu
- Rahoton FMDQ ya ce an siyar da dala a ranar Juma'a 17 ga watan Mayu kan N1,497 idan aka kwatanta da N1,533 a ranar Alhamis 16 ga watan Mayu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Bayan shan duka a wurin dala, Naira ta sake farfaɗowa karo na biyu a cikin mako daya.
Darajar Naira ta fadi har tsawon makwanni biyu bayan kasancewa daga cikin kudi da ke inganta a duniya.
Yanayin farashin Naira a kasuwanni
A ranar 17 ga watan Mayu ana siyar da dala kan N1,497 idan aka kwatanta da N1,533 a ranar Alhamis 16 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan a kasuwannin bayan fage, ana siyar da dala kan N1,480 madadin N1,540 a ranar Alhamis 16 ga watan Mayu.
Hakan ya nuna cewa darajar ta karu da kusan N100 kenan kamar yadda rahoton FMDQ ta bayyana.
Musabbabin tashin Naira a kwanakin baya
Hakan kamar yadda masana ke cewa bai rasa nasaba da tsare-tsaren da Babban Bankin CBN ya kawo.
A rahoton FMDQ ta ce a ranar 17 ga watan Mayu an sami hada-hadar dala da ya kai $83.5m wanda ya ragu da 69% kenan idan aka kwatanta da $272m a kwanakin bayan.
Naira ta sake galaba kan dala
A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa bayan shan bugu da Naira ta yi a hannun dala ta sake farfaɗowa a kasuwa.
Naira ta kara yin sama da kusan kaso 4.04 a yayin cinikayya a kasuwar ƴan canji kamar yadda rahoton FMDQ ya nuna.
Hakan ya nuna Naira ta karu da N61 a kasuwanni bayan shafe kusan makwanni biyu ta na yin kasa a kasuwa.
Asali: Legit.ng