Peter Obi Ya Bayyana Babbar Matsalar Dimokradiyya a Najeriya

Peter Obi Ya Bayyana Babbar Matsalar Dimokradiyya a Najeriya

  • 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labor a shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana babbar matsalar da Najeriya ke ciki
  • Peter Obi ya ce a halin yanzu kotuna da alkalai sune manyan barazana ga dimokuraɗiyyar da al'ummar tarayyar Najeriya
  • Legit ta tattauna da wani masanin harkokin sharia', Marwan Abdulhakam kan jin matsayin maganar da Peter Obi ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya nuna shakku kan alkalai a Najeriya.

Peter Obi
Peter Obi ya zargi kotuna kan lalacewar Najeriya. Hoto: Mr. Peter Obi.
Asali: Facebook

Peter Obi ya tabbatar da cewa matsalar zabe a Nigeria alkalai ne ke jawo ta ba hukumar zabe ta kasa ba.

Kara karanta wannan

'Mutane 4 aka sace ba 500 ba,' DHQ ta yi bayani kan satar mutanen Zamfara

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Peter Obi ya yi jawabin ne a wani taro a jami'ar Godfrey Okoye da ke jihar Enugu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi: Ya kamata a gyara kotuna

Peter Obi ya ce lallai akwai bukata ta musamman kan kawo gyara a kan yadda alkalai ke gudanar da ayyukansu a Najeriya.

Ya ce hakan ya zama dole lura da yadda kowane dan kasa ya dogara a kan kotuna wajen neman hakki, rahoton Vanguard.

'INEC ba ta da laifi' Inji Obi

Peter Obi ya yi karin haske kan yadda yan Najeriya ke kuka kan hukumar zabe ta kasa (INEC) a lokacin zabuka.

Ya ce duk lokacin da ake magana kan lalacewar dimokuraɗiyya al'umma suna daura laifi ne ga hukumar INEC amma ba su ne da laifi ba.

...A ina Peter Obi ya hango matsalar?

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Ka yi hankali da mutanen Arewa, Ibo sun fara gargadin Peter Obi

A cewar Peter Obi, kotuna su ne babbar barazana ga yan Najeriya a halin yanzu saboda ba sa kare hakkin al'umma yadda ya kamata.

Ya kara da cewa a yanzu kotuna sun zama tamkar haja a kasuwa, idan kana da kudi za ka iya sayan duk wacce kake so.

Saboda haka ya yi kira kan gyara na musamman a harkar alkalanci idan ana son kawo cigaba a Najeriya.

Legit ta tattauna da Marwan Abdulhakam

Biyo bayan maganganun da Peter Obi ya yi, Legit ta tattauna da wani masanin shari'a kan jin yadda doka za ta kalli maganganun.

Marwan Abdulhakam ya ce maganar da Peter Obi ya yi ta na kan kuskure domin duk hukuncin da kotu ta yanke shine daidai.

Peter Obi ya ziyarci Atiku Abubakar

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labor, Peter Obi ya magantu kan ziyarar da ya kai wa jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP.

Peter Obi ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bukola Saraki da Sule Lamido domin tattaunawa kan harkokin siyasa da makomar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng