Kaso 80 cikin 100 na malaman makarantun jihar Nasarawa dakikai ne - Gwamna Al-Makura
- Kaso 80 cikin 100 na malaman makarantun jihar Nasarawa dakikai ne inji Gwamna Al-Makura
- Gwamnan ya bayyana hakan ne a garin Akwanga, na jihar a jiya Litinini
- Gwamnan ya samu wakilcin kwamishinan Ilimi na jihar ne Alhaji Tijjani Aliyu Ahmad
Akalla kaso 80 cikin 100 na malaman dake koyarwa a makarantun gwamnati na jihar Nasarawa basu da cikakkiyar kwarewa akan aikin da suke yi inji gwamnan jihar ta Nasarawa, Alhaji Tanko Al-Makura.
KU KARANTA: An dawo da gawar Alex Ikweme gida don biznewa
Gwamnan ya bayyana hakan ne a garin Akwanga, na jihar a jiya Litinini inda kuma ya sake bayyana cewa idan har gwamnatin sa zata yi jarabawa ga malaman kamar yadda akayi a jihar Kaduna, to tabbas da yawan su ba za su ci ba.
Legit.ng ta samu dai cewa Gwamnan ya samu wakilcin kwamishinan Ilimi na jihar ne Alhaji Tijjani Aliyu Ahmad a warin wani taron lalubo hanyoyin gyara ga kundin koyo da koyarwa na kasar.
A wani labarin kuma, Babban bankin Najeriya na CBN a jiya litinin ya sake zuba akalla $210 miliyan a cikin kasuwannin canji daban-daban da ke gare mu a kasar nan da nufin kara farfado da darajar Naira tare da daidaituwar lamurran kasuwar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng