Kamfanin Hada Hadar Kudi Na Nigeria Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 11, an Yi Masa Kutse
- Kamfanin fasahar hada-hadar kudi na Flutterwave, ya sake gamuwa da sharrin masu kutse, inda ya tafka asarar Naira biliyan 11
- Ana zargin an rarraba kudin da aka satar wa Flutterwave zuwa wasu asusun banki da kuma cibiyoyin hada-hadar kudi
- Sai dai Flutterwave ya ce kutsen da aka yi wa kamfanin tare da wawure biliyoyin Naira bai shafi kuɗin abokan huldarsa ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katafaren kamfanin Flutterwave na Najeriya ya sake gamuwa da sharrin 'yan yahoo, inda suka yi masa kutse tare da wawure Naira biliyan 11 zuwa asusun banki daban-daban.
Lamarin ya faru ne wata guda bayan da kotu ta umarci Flutterwave da ya dawo da wasu Dala miliyan 24 da masu kutse suka wawure na abokan huldarsa ta hanyar na'urar PoS.
An tura kudin zuwa asusu daban-daban
Rahotan jaridar Tech Cabal ya bayyana cewa barayin sun tura Naira biliyan 11 (kimanin dala miliyan 7) zuwa wasu asusu daban-daban a cikin watan Afrilun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya mai tushe ta ce an tura kudin zuwa asusu daban-daban a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi guda biyar cikin kwanaki hudu.
Kamfanin Flutterwave ya magantu
Kamfanin ya bayyana cewa ya ga lokacin da masu kutsen ke farmakar dandalin nasu, sai dai kafin su farga, aikin gama ya gama, jaridar The Punch ta ruwaito.
Flutterwave bai bayar da wani karin bayani kan irin barnar da masu kutsen suka yi ba amma ya tabbatar da cewa babu kudin wani abokin hulda da zai yi ciwon kai.
Flutterwave ya ce:
"Wannan ba bakon abu ba ne a masana'antar hada-hadar kudi ta intanet, a kullum masu kutse na kokarin lalata tsaro na shafukan kamfanoni domin satar kudi ko bayanai.
Hukumar FIRS ta tattara harajin N3.94trn
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS) ta tara harajin Naira tiriliyan 3.94 a watanni ukun farko na shekarar 2024.
Shugaban FIRS, Zacch Adedeji wanda ya bayyana adadin kudin a ranar Alhamis a Abuja, ya ce suna son tara Naira tiriliyan 19.4 zuwa karshen 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng