Majalisar Dattawa Ta Zartar da Kudurin Kafa Hukumar Raya Jihohin Arewa Maso Yamma

Majalisar Dattawa Ta Zartar da Kudurin Kafa Hukumar Raya Jihohin Arewa Maso Yamma

  • A ranar 16 ga watan Mayu, majalisar dattawa ta zartar da kudurin doka na kafa hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC)
  • An zartar da kudurin dokar ne bayan shugaban kwamitin ayyuka na musamman, Sanata Kaka Shehu ya gabatar da rahoto a kai
  • Mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau ya yi na'am da wannan rahoto, wanda aka zartar da shi domin farfado da shiyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta zartar da kudurin doka na kafa hukumar raya jijohin yankin Arewa maso Yamma.

Majalisar ta zartar da wannan kudurin dokar ne a ranar Alhamis bayan Sanata Kaka Shehu, shugaban kwamitin ayyuka na musamman ya gabatar da rahoto kan kudurin.

Kara karanta wannan

Dan majalisar PDP ya nemi Tinubu ya fara tafiye tafiye a mota ko ya hau jirgin haya

Majalisar dattawa ta zartar da kudurin dokar kafa hukumar NWDC
Majalisar Dattawa ta zartar da kudurin dokar kafa hukumar Arewa maso Yamma. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Sanata Shehu ya nemi a zartar da kudirin

Jaridar The Cable ta ruwaito Sanata Kaka Shehu ya bayyana wa majalisar cewa kudurin zai bunkasa tattalin arzikin Arewa maso Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Sanata Shehu:

"Manufar gabatar da wannan kudurin shi ne bullo da hanyoyin inganta rayuwa da bunkasa tattalin arziki shiyyar Arewa maso Gabas.
"Lallai akwai bukatar majalisar dattawa ta zartar da wannan kudurin doka."

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa majalisar ta yi nazari kan rahoton, inda mataimakin shugaban majalisar, Sanata Jibrin Barau ya yi jawabi.

Ta'addaci ya gurgunta Arewa maso Yamma

Sanata Barau ya ce:

"Mun gamsu da bukatar da ke da akwai na gyara ababen more rayuwa a shiyyar. Muna fatan wannan rahoton zai samu karbuwa a wajen majalisar wakilai.
"Kowa ya san yadda ta'addancin 'yan bindiga da Boko Haram ya lalata shiyyar, gine-gine da dama sun lalace, uwa uba kuma nan ne cibiyar samar da abinci a kasar."

Kara karanta wannan

Shugaban APC Ganduje zai sarara bayan kotu ta dakatar da bincikensa

Bayan kafa hukumar raya yankin Niger Delta (NDDC) da na Arewa maso Gabas (NEDC), sauran shiyyoyi ke fafutukar ganin su ma an kafa ta su hukumar.

Majalisa ta magantu kan jirgin shugaban kasa

A safiyar yau Alhamis, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta tafka muhawara kan yawan lalacewar jiragen fadar shugaban kasa da kuma yadda Bola Tinubu ke hawa jirgin 'yan kasuwa.

A zaman majalisar, Hon. Ali Isa, ya kawo shawarar cewa shugaban kasar ya fara yin tafiye-tafiye a mota ko a ya ci gaba da hawa jirgin 'yan kasuwa tunda na gwamnati na da matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel