Naira Ta Sake Samun Galaba Kan Dala Bayan Ƙaruwa da 4.04% a Kasuwa
- An samu ci gaba a kasuwar ƴan canji bayan Naira ta sake farfaɗowa da kusan 4.04% a jiya ranar Laraba 15 ga watan Mayu
- Ana siyar da Naira kan farashin kudi N1,459 a jiya Laraba 15 ga watan Mayu idan aka kwatanta da farkon makon da muke ciki
- Wannan ya nuna Naira ta samu karin N61 kenan kan dala idan aka kwanta da N1,520 da aka siyar a ranar Talata a kasuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da Naira ta sha fama a kwanakin nan, ta sake farfaɗowa a jiya Laraba 15 ga watan Mayu.
Darajar Naira ya sake tashi da kusan N61.38 inda ake siyar da ita N1,459 kan kowace dala a kasuwa.
Naira ta ƙaru da 4.04% kan Dala
Wannan na kunshe a cikin wani rahoto da hukumar cinikayyar kudi ta FMDQ ta fitar a jiya Laraba 15 ga watan Mayu, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya nuna darajar Naira ya karu da 4.04% idan aka kwatanta da ranar Talata 14 ga watan Mayu da aka siyar da naira N1,520, cewar rahoton Vanguard.
Har ila yau, an samu karin hada-hadar dala da yawa da ya kai $298m a jiya Laraba 15 ga watan Mayu idan aka kwanta da $128m a ranar Talata 14 ga watan Mayu.
Naira ta sha wahala a hannun Dala
Wannan na zuwa ne bayan cin karo da matsaloli da Naira ke yi a kasuwa musamman faduwar darajarta.
A cikin kwanakin nan Naira ta ci gaba da faduwa idan aka kwatanta da dala wanda ya jefa tsoro a zukatan ƴan Najeriya.
Naira ta sake faduwa a kasuwa
A wani labarin, Ƙimar Naira ya ƙara faɗuwa a kasuwar gwamnati yayin da aka yi musaya kan N1,466.31/$ ranar Jumu'a 10 ga watan Mayu.
Rahotannin sun tabbatar da cewa farashin musayar Dala zuwa Naira ya karu da N40 tsakanin ranar Alhamis da Juma'a inda ya tashi daga N1,426/$.
Kasuwar hada-hadar musayar kuɗin ƙasashen waje ta ƙasa (NAFEM) ta tabbatar da tashin Dala a tsakanin ranar Alhamis da Jumu'a na makon jiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng