Tsadar Rayuwa: An Samu Tashin Farashin Kayan Masarufi da 33.69% a Watan Afrilu

Tsadar Rayuwa: An Samu Tashin Farashin Kayan Masarufi da 33.69% a Watan Afrilu

  • Duk da saukan farashin dala a watan Afrilu da ya gabata, bincike ya nuna cewa an samu karin tashin farashin kayan masarufi
  • Cibiyar kididdiga ta (NBS) ta fitar da jadawalin hauhawar farashin kayan masarufi cikin shekarar 2023 zuwan watan Afrilun 2024
  • Hauhawar farashin ya shafi kayan masarufi kamar su shinkafa, wake, masara, doya, taliya, garin kwaki, kayan marmari da kayan shayi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Duk da saukar farashin dala a watan Afrilun wannar shekarar ta 2024, an samu tashin farashin kayyakki da kashi 33.69%.

Farashin kayayyaki
Farashin kayan masarufi ya tashi a watan Afrilu duk da saukar farashin dala. Hoto: Hoto: Emmanuel Osodi/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Bayanan da cibiyar kididdiga ta kasa (NBS) ya nuna cewa an samu tashin farashin kayayyaki a watan Afrilu da ya gabata.

Kara karanta wannan

‘Yan kasuwa sun fara saida fetur a sabon farashi yayin da lita ta koma N770 a depo

Yadda farashin kayayyaki ya tashi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa farashin kayayyaki ya karu ne a watan Afrilu da kashi 0.49% idan aka kwatanta da watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangaren farashin kayan abinci kuwa idan aka kwatanta watan Afrilun 2023 da na shekarar 2024 an samu kari sosai.

A watan Afrilun shekarar 2023 tashin farashin ya kasance bisa 24.61% amma ya haura zuwa 40.53% a watan Afrilun 2024.

Nau'in kayayyakin da suka tashi

Kayan abincin da suka kara kudi sun hada da shinkafa, gero, wake, masara fulawa, dawa, burodi da kayan shayi, rahoton the Cable ya tabbatar da wannan.

Har yanzu dai sun haɗa da man gyada, man ja, madara, doya, taliya, garin kwaki, nama, kifi da kayan marmari.

Duk da samun tashin farashin, idan aka kwatanta watan Maris da Afrilu na shekarar 2024, farashin ya sauka da kashi 1.11% a watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Kayayyaki za su kara tsada a Najeriya, an kara harajin shigo da kayan kasar waje

Hakan kuma ya jawo saukan farashin wasu kayan masarufi da kaso kadan a wasu kasuwanni a fadin Najeriya.

Farashin kaya ya sauka kadan

A wani rahoton, kun ji cewa farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa, sukari, fulawa, taliyar indomi da dai sauran su ya fara sauka a kasuwannin Najeriya.

Wannan kuwa ya faru ne sakamakon darajar da Naira ta yi a kan Dalar Amurka da ma sauran kudaden kasashen waje. Ana hasashen farashin kayayyaki zai ci gaba da faduwa yayin da Naira ta ke kara daraja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng