Majalisa Ta Amince Gwamnati ta Karbo Bashin $500m a Magance Matsalar Wuta

Majalisa Ta Amince Gwamnati ta Karbo Bashin $500m a Magance Matsalar Wuta

  • Majalisar dattawa ta amincewa gwamnatin tarayya ta ranto $500m domin sanya mitar wuta a gidajen ‘yan Najeriya yayin da ake matsalar wuta
  • Hukumar da ke lura da sayar da kadarorin gwamnati (BPE) ce za ta mikawa makudan kudin domin ta tabbatar da an sayo mitar da za a rarraba ga 'yan kasa
  • Ministan makamashi, Cif Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ‘yan Najeriya miliyan 92 ne ba su da mita, yayin da aka samu karuwar masu sanya mita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Majalisar dattawan ta sahalewa gwamnatin tarayya ta ciyo rancen $500m a kokarin da ake yi na tabbatar da cea dukkanin ‘yan Najeriya su na da mitar wuta.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Hukumar da ke lura da sayar da kadarorin gwamnati (BPE) ce za ta yi amfani da kudin wajen sayen mita da za a raba a gidajen jama'a.

Ministan hasken wuta
An amincewa gwamnatin tarayya ta ranto $500m domin sanya mita a gidajen 'yan Najeriya Hoto: @federal_power
Asali: Twitter

Nigerian Tribune ta walllafa cewa Ministan hasken wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ‘yan Najeriya miliyan 92 ne ba su da mita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miliyoyi ba su da mitar wuta

Akalla mutane kimanin miliyan 7.4 ne ke rayuwa ba tare da sun mallaki mita ba duk da cewa an samu karin wadanda su ka sanya mitar da kaso 5%.

Vanguard News ta wallafa cewa mutane kimanin 179,792 su ka sanya mitar a shekarar 2024, idan aka kwatanta da shekarar 2023 da mutane 171,107 su ka sanya mitar a gidajensu, kamar yadda hukumar kula da hasken wutar lantarki ta ce.

A cewar Ministan kula da hasken wuta, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa akalla mutane kamfanin rarraba hasken wuta ta Ikeja a jihar Lagos ta raba kimanin kaso 73% ga abokan huldarsa.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa dalibar da aka ci zalinta a makarantar Abuja ke neman diyyar N500m

Shi kuma kamfanin rarraba hasken wuta da ke Abuja ya raba kaso 61% ta raba ga abokan huldarsa, kamfanin Eko kuma ya raba kaso 59%.

An nemi Ministan wuta ya yi murabus

Mun ba ku labarin cewa wasu matasa musamman a Arewacin Najeriya sun taso Ministan hasken wutar lantarki gaba a kan sai ya ajiye mukaminsa.

Wani lauya a jihar Taraba, Bilyaminu Maihanchi da ke daya daga cikin wadanda su ka yi kiran ya bayyana cewa ministan ya gaza wajen magance matsalar wutar lantarki da yankin ke fuskanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.