'Sannu a Hankali za mu Bincike Shi', EFCC Tayi Magana Kan Ministan Tinubu
- Wasu matasa sun yi zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja su na bukatar hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta binciki Bello Matawalle
- Ana dai zargin tsohon Gwamnan jihar Zamfara, kuma karamin Ministan tsaro a yau, Bello Matawalle da almundahanar N70bn daga shekarar 2019 zuwa 2023
- Hukumar EFCC ta nanata cewa sannu a hankali za ta ci gaba da binciken Ministan, tare da tabbatarwa da matasan cewa ba za su yi wasa da aikinsu na bincike ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta bayar da tabbacin cewa sannu a hankali ta ke ci gaba da bincikar zargin almundahanar N70bn da ake yiwa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale ne ya bayyana matakin EFCC yayin wata ganawa da kungiyar matasa da mata da ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar ta dade tana neman hukumar EFCC ta gaggauta binciken zargin almundahana da ake yiwa tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC: Zanga-zanga kan Bello Matawalle
Wasu matasa sun yi zanga-zanga su na neman hukumar EFCC ta binciki karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Ana zargin Matawalle da wawashe kudin al'ummar Zamfara daga shekarar 2019-2023 da ya mulki jihar.
EFCC ba ta manta da Matawalle ba
Ko a mako biyu da su ka wuce, sai da EFCC ta nanata cewa ba za ta manta da binciken Bello Matawalle ba, kamar yadda Leadership News ta wallafa.
An gano wasu daga matasan na rike da kwalaye su na tunatar da EFCC da kada ta manta da binciken Matawalle.
Hukumar EFCC na binciken Yahaya Bello
A baya mun ba ku labarin cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'adi (EFCC) ta fara binciken tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello bisa zargin almundahana.
Daga tuhumar da EFCC ke yi wa Yahaya Bello akwai amfani da kudin jama'a wajen biyan kudin makarantar dansa, da kuma sama da fadi da kudin mutanen jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng