Bayan Kashe Sojoji, Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Sama da 80 a Katsina

Bayan Kashe Sojoji, Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Sama da 80 a Katsina

  • Yan bindiga sun sake kai hari kauyen Ƴar-Malamai a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina jim kaɗan bayan jami'an tsaro sun bar garin
  • Mazauna kauyen sun bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da mutane sama da 80, sun ƙona gidaje tare da sace kayan abinci
  • Har yanzun babu wata sanarwa a hukumance amma rundunar sojoji ta tabbatar da kashe jami'anta huɗu ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 80 a ƙauyen Yar-Malamai da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan ƴan bindigar sun yi ajalin sojoji a wani sansanin sojoji da ke yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 50, sun sace mutane sama da 500 a Arewa

Gwamma Dikko Radda.
'Yan bindiga sun sake komawa yankin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Wani mazaunin yankin ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa ƴan ta'addan sun sake komawa ƙauyen ranar Litinin, suka yi awon gaba da mutane sama da 80.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun tafka ɓarna a Katsina

Ya bayyana cewa maharan sun kuma fasa shaguna sun kwashi kayayyaki, sannan sun ƙona gidaje a harin wanda ya shafe kusan sa'o'i 10.

“Yan bindigar sun sake kai hari kauyen inda suka saci kaya a shaguna, suka kona gidaje da ababen hawa, suka kuma yi awon gaba da jama’a da dama bayan tafiyar sojoji," in ji shi.

Wani mai riƙe da muƙamin siyasa a yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yawan hare-haren ya sa mutane sun tashi daga kauyen.

Mazuna Ƴar-Malamai sun tashi

“A yanzu haka gidaje shida ne suka rage a tsaye a ‘Yar-Malamai. ‘Yan bindigar sun yi garkuwa da mutane kusan 80 yawancinsu mata tare da sace kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi musayar wuta da ƴan bindiga, sun samu gagarumar nasara a Katsina

"Muna cikin mawuyacin hali kuma muna buƙatar abinci da wurin kwana. Muna rokon gwamnati da ta taimaka mana ta kowace hanya.
"Bayan kashe sojoji da dan banga tare da raunata wasu, jami’an tsaro suka tattara suka bar garin, ‘yan sa’o’i kadan bayan haka ‘yan bindigar suka dawo, suka kona gidaje da motoci tare da sace mata."

- In ji ɗan siyasar.

An kashe sojoji a Katsina

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko rundunar sojoji dangane da sabon harin.

Amma rundunar soji a ranar Talata ta tabbatar da kashe sojoji hudu a karamar hukumar Faskari ta Katsina a ranar Lahadi, cewar rahoton Leadership.

Ƴan bindiga sun tashi kauyuka 50

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun tarwatsa mutane a kauyuka 50 a ƙaramar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a Arewa maso Yamma.

Mamba mai wakiltar Zurmi da Shinkafi a majalisar wakilai ta ƙasa, Bello Hassan ya ce ƴan bindiga na kai hari kan jama'a ba dare ba rana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel