Kotun Ingila Ta Yanke Wa Ɗan Najeriya Hukunci Bisa Laifin Kashe Matarsa

Kotun Ingila Ta Yanke Wa Ɗan Najeriya Hukunci Bisa Laifin Kashe Matarsa

  • Kotun Burtaniya ta yanke wa ɗan Najeriya, Olubunmi Abodunde hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan kama shi da laifin kashe matarsa
  • Alkalin kotun ya bayyana cewa magidancin zai shafe shekaru 17 a gidan yari kafin ya samu damar da za a iya bada belinsa na ɗan lokaci
  • Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da aka fitar da sakamakon gwajin da aka yi wa gawar matar da aka kashe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kotun Ipswich a ƙasar Burtaniya ta yankewa ɗan Najeriya, Olubunmi Abodunde, hukuncin ɗaurin rai da rai bisa kama shi da laifin kisan matarsa, Taiwo Abodunde.

Bayan gwajin gawar da aka yi, kotun ta gano cewa wanda ake zargin ya buga wa marigayyar allo a kai, har ya yi mata rauni a kwakwalwa.

Kara karanta wannan

"Ban da hannu":Ɗan El-Rufai ya faɗi gaskiya kan kwangiloli a mulkin mahaifinsa a Kaduna

Olubunmi Abodunde da matarsa.
Kotu ta kama ɗan Najeriya da laifin kashe matarsa a ƙasar Burtaniya Hoto: Olubunmi Abodunde
Asali: Instagram

Gwajin ya kuma nuna cewa an taɓa shaƙe marigayiyar mai ƙaramin ƙarfi a wani faɗa mai muni da suka yi tun a watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Abobunde ya zama ajalin matarsa

Kafin faruwar lamarin, kotu ta haramtawa Mista Abodunde zuwa gidan matarsa, bayan da aka samu rahotannin cin zarafi da yake yawan yi mata, Vanguard ta ruwaito.

Amma ya sa ƙafa ya shure umarnin kotun, inda ya koma gidan da sunan ya je ɗauko wayarsa ta hannu.

A bidiyon da kamarar foCCTV ta ɗauka, magidancin ya shiga gidan kuma ya jima kusan mintuna 30, wanda ya sa ake tunanin ya zauna ne yana jiran dawowar matar.

Rahotanni sun nuna cewa ma'auratan sun yi faɗa a lokacin kan wanda zai riƙa sauke nauye-nauye da kuma zargin cin amana, lamarin da ya sa aka kama mutumin a lokacin.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnan PDP ya ɗauki zafi, ya sha alwashin bincikar Ministan Bola Tinubu

Daga bisa aka ba ɗa belinsa bisa sharaɗin cewa ba zai sake sa ƙafa a gidan da take zaune ba, Sahara Reporters ta ruwaito.

Yadda ɗan Najeriya ya kashe matarsa a Ingila

A ranar da suka yi faɗa tsakaninsu, ƴan sanda biyu sun je gidan domin tattaunawa da matar kan abin da ya haɗa ta sa'insa da mai gidanta.

Mai gabatar da kara, Stephen Spence KC, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ne kadai zai iya faɗin ainihin abin da ya faru.

"Jami'an ƴan sanda sun kwankwasa ƙofa lokacin da suka isa gidan amma suka ji shiru kuma babu wata alamar ana neman taimako daga ciki," in ji Mista Spence.

Ƴan sandan ba su ɓalle kofar ba saboda dole sai da izinin hakan, wanda daga bisani suka samu izinin kuma daga shiga suka tarar da gawar Misis Abodunde.

Amma da yake kare kansa, magidancin ɗan asalin Najeriya ya shaidawa kotun cewa a lokacin da ya aikata ɗanyen aikin ya ɗan sha magunguna.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta matashi mai karyar ya shigo musulunci daga Kiristanci a Kano

An samu tsaiko a shirin gurfanar da Sirika

A wani rahoton kuma Hukumar EFCC ta gamu da matsala yayin gurfanar da Hadi Sirika da ɗan uwansa a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

An tsara fara sauraron shari'ar tsohon ministan kan tuhumar karkatar da kudin kwangila N19.4bn amma bai samu halarta ba saboda kuskuren EFCC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel