Gwamnatin Kano Ta Yi Magana a Kan Rahoton Bullar Rashin Tsaro a Jihar
- Gwamnatin Kano ta bayyana rahoton cewa akwai rashin tsaro a jihar a matsayin labaran karya da bai dace a rika yadawa ba ganin yadda ake zaman lafiya
- Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya musanta labarin a ranar Litinin, inda ya ce akwai rashin adalci a yada babu tsaro a Kano
- Ya ce Kano na daga jihohi mafi ingantaccen tsaro a tarayyar Najeriya, da ma yankin Afrika ta yamma, saboda haka kowa ya shigo ya yi kasuwanci ba tare da tsoro ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano-Gwamnatin Kano ta ta musanta labarin cewa akwai matsalar rashin tsaro a jihar kamar yadda wasu rahotanni ke bayyanawa.
Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya musanta zargin a ranar Litinin, inda ya ce rashin adalci ne a ce babu zaman lafiya a Kano.
Akwai matsalar tsaro a jihar Kano?
Kwamered Aminu AbdulSalam Gwarzo ya bayyana haka ne yayin bikin bude makon shari’a a shekarar 2024, kamar yadda Leadersip News ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
“Kano na daga wurare mafi tsaro a Najeriya, ko ma Afrika ta yamma.”
“Akwai tsaro a Kano,” Kwamred AbdulSalam
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa kano wuri ne da kowa ya kamata ya shigo ba tare da jin dar-dar a zuciyarsa ba.
Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda ya ce Kano wuri ne da ya kamata a shigo domin yin kasuwanci, kuma yayata labarin babu tsaro a jihar rashin adalci ne.
Ko a baya rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa ta na sintiri a iyakokin jihar domin tabbatar da tsaro, da hana bata-gari tsallakowa jihar, kamar yadda Punch News ta wallafa.
Mataimakin gwamnan ya ce labarin rashin tsaro a Kano labaran karya ne kawai, kuma bai dace a dinga yayata wannan labarin marar dadin ji ba.
An kama ‘yan daba 61 a Kano
A baya mun ba ku labarin cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan daba kimanin 61 da su ka addabi jihar.
An kama ‘yan daban ne a sassan masarautun jihar guda biyar a daidai lokacin da ake ci gaba da bukukuwan sallah karama a fadin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng