Operation Kauda Badala: Hisbah ta Damke Maza da Mata 20 Suna Wanka Tare a Kano

Operation Kauda Badala: Hisbah ta Damke Maza da Mata 20 Suna Wanka Tare a Kano

  • Hukumar hisba a Kano ta bayyana kama wasu matasa 20 da suka addabi mazauna titin ringroad a jihar bayan an tseguntawa jami’an hukumar cewa ana aikata badala a wurin
  • Ana zargin matasan maza da mata da rashin ta ido inda su ka shiga wani gidan shakatawa suna wanka tare, lamarin da hukumar ta ce ba za ta lamunta ba
  • Mataimakin Kwamanda a hukumar, Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar ya ce laifin ya saba da dokar addinin musulunci, kuma ba karamin zunubi suka aikata ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Jami’an hisba a jihar Kano sun cafke wasu matasa guda 20 da ake zargi da aikata badala a wani gidan shakatawa dake titin ring road wanda hakan ya damu mazauna yankin matuka.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Jami’an da ke aiki da bangaren ‘operation kauda badala’ sun kama matasan ne bayan mazauna unguwar sun shigar da kokensu kan yadda ake bata musu unguwa da mummunan aiki.

Shugaban hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
An cafke matasa 20 suna wanka tare a Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Mataimakin kwamandan hukumar, Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya bayyana cewa ba karamin laifi matasan su ka aikata ba, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar ya yi karin bayanin cewa iyo da zummar shakatawa da matasan su ka yi bai dace ba, kuma da wani aikin ladan su ka yi da ya fiye musu duniya da gobe kiyama.

Hisba za ta hukunta wasu matasa

Hukumar hisba da ke umarni da kyakkyawa da hani da mummunan aiki a jihar Kano ta yi kakkausan tsawatarwa kan matasan da ke murje idanunsu suna aikata ayyukan da musulunci ya yi hani da su.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Ya bayyana cewa hukumarsu na binciken wasu matasa 20 da ake zargi da aikata badala a titin Ring Road da ke jihar. Ko a baya hukumar ta cafke wasu mata da laifin sata kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Dr. Aminuddin ya ce da zarar an kammala binciken za a hukunta matasan dai-dai da laifuffukan da ake zargin sun aikata.

Shugaban ya ce wajibin iyaye ne su sanya idanu kan yaransu da abokanan huldarsu domin tsaftace tarbiyyarsu.

Daurawa ya koma shugabancin Hisbah

A baya mun kawo muku labarin cewa Sheikh Dr. Aminu Ibrahim Daurawa ya koma shugabancin kujerarsa ta shugaban hisba.

Wannan na zuwa ne bayan Sheikh Daurawa ya bayyana ajiye aikinsa bayan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya fito ya nuna gazawar hukumar hisba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel