Aiki Ba Lasisi: Kotu Ta Yanke Hukuncin Dauri Kan ’Yan Canji 17 da Aka Kama a Kano
- Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano, ta yanke wa wasu 'yan canji 17 hukuncin zaman gidan yari na watanni shida
- Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa ya kuma ba kowannensu zabin biyan tarar N50,000 yayin da yake yanke hukunci
- An ruwaito cewa jami'an DSS da ‘yan sanda ne suka kama mutanen 17 bisa zargin gudanar da ayyukan canji ba bisa ka’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa na babbar kotun tarayya ya yankewa wasu 'yan canji 17 a jihar Kano hukuncin zaman gidan yari na watanni shida.
Kotun ta daure 'yan canjin ne saboda sun gudanar da kasuwanci ba tare da lasisin da ya dace ba, wanda ya saba wa sashe na 57 (5) (b) na dokar bankuna da cibiyoyin kuɗi ta 2020.
Hukuncin daurin wata 6 ko tarar N50,000
An yanke wa kowane mai laifin hukuncin daurin watanni shida ko kuma biyan tarar N50,000, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Ayuba Ibrahim, Idris Saidu, Idris Usman, Shuaibu Muhammad, Hamisu Ilyasu da wasu mutum 12.
An yanke masu hukuncin ne bayan da suka amsa laifin tuhuma daya da ake yi masu a lokacin da ake karanta masu shari'ar.
Wannan dai na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ke kara matsin lamba kan 'yan canji a fadin Najeriya a wani yunkuri na daidaita farashin Naira a kasuwar canji
Jami'ai sun kai samame kasuwar Wapa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 17 a kasuwar Wapa da ke Fagge, bisa zargin su na gudanar da ayyukan canji ba bisa ka’ida ba.
A ranar Laraba ne kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Usaini Gumel, ya ce an kama mutane 29 tare da kwato CFA 68,000, da Rufi 30, amma daga bisani aka wanke mutum 12.
Kwamishinan ƴan sandan ya yabawa rundunar hadin guiwa ta 'yan sanda da jami'an hukumar DSS bisa jajircewa da hadin kai wajen ganin an samu nasarar wannan aikin.
Asali: Legit.ng