Rusau a Abuja: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin Aniyar Rushewa ’Yan Kasuwa Shaguna 500
- Hukumar kula da birnin tarayya Abuja (FCDA) ta sanar da fara ayyukan rusau kan wasu shaguna da aka gina ba bisa ka'ida ba
- Jami'in hukumar, Garba Jibril ya tabbatar da cewa za a rusa shaguna 500 ne domin suna kawo tsaiko kan ayyukan cigaba a babban birnin
- Malam Garba Jibril ya kuma bayyana irin kokarin da hukumar ta yi wurin fadakar da masu shagunan tun a karon farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Hukuma mai kula da cigaban birnin tarayya Abuja (FCDA) ta bayyana aniyar ta na fara yin rusau.
Legit ta gano haka ne cikin wata sanarwa da hukumar ta ba wasu masu shugaba wa'adin sa'o'i 24 domin su tashi.
Adadin shagunan da FCDA za ta rusa
Rahoton da jaridar Aminiya wallafa ya nuna cewa shagunan da hukumar za ta rushe a karon farko sun kai 500.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shagunansu 500 suna kan hanyar Karmo ne zuwa Dei-Dei kamar yadda rahotanni suka tabbatar a makon nan.
Jawabin jami'in FCDA kan rusau a Abuja
Wani jami'in hukumar FCDA, Garba Jibril ya tabbatar wa manema labarai cewa hukumar ta ja kunnen masu shagunan da dadewa.
A cewarsa, dukkan jan kunne da hukumar tayi musu kan gina shagunan ba su hanu ba, cewar rahoton Pulse Nigeria.
Ya kuma kara da cewa tun a karon farko aka tabbatar musu da cewa za a rushe ginin da ba bisa ka'ida aka yi shi ba.
Daraktan FCDA ya zauna da masu shaguna
Babban daraktan hukumar, Mukhtar Galadima ya yi zama da masu shagunan domin yi musu nuni kan muhimmancin aikin.
Malam Mukhtar Galadima ya ce shagunan sun saba da tsarin birnin kuma za su hana kawo cigaba.
Sannan ya kara da cewa akwai aikin titin da za a yi a wurin amma zaman shagunan ya hana fara aikin.
Wike ya yi rusau a Abuja kwanaki
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa (DRTS), a babban birnin tarayya ta fara rusa gidajen cin abinci, shaguna, da sauran gine-gine da basa bisa ka'ida. .
Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara aikin rusau daga Area 3 da Banex Junction da yankin Area 3. Tawagar DTRS, tare da taimakon hukumomin tsaro ne suka rusa wuraren.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng