Wata Bakuwar Cuta Ta Yi Sanadiyyar Ajalin Mutane Sama da 10 a Jihar Zamfara

Wata Bakuwar Cuta Ta Yi Sanadiyyar Ajalin Mutane Sama da 10 a Jihar Zamfara

  • An samu karuwar adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar bakuwar cutar da ta bulla jihar Zamfara kwanan nan
  • Cutar ta bulla ne a wasu yankunan kananan hukumomin Maradun, Zurmi, Shinkafi da wani yankin Sokoto
  • Gwamnatin jihar ta bayyana alamomin da ake gane cutar da matakan da suka dauka domin dakile yaduwarta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Adadin waɗanda suka mutu sakamakon bakuwar cutar da ta bulla wasu yankunan jihar Zamfara sun karu.

Jihar Zamfara
Mutane 13 sun mutu, da dama suna asibiti sanadiyyar bakuwar cuta a Zamfara. Hoto: @Mfareees
Asali: Twitter

Cutar wacce ta fi shafar yara ƙanana da mata ta kashe mutane 13 a wurare mabanbanta a halin yanzu.

Yankunan Zamfara da aka fi samun cutar

Binciken da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa cutar ta kama mutane 505 a Maradun, Shinkafi da Gusau.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama yan bindiga da matsafi da gashin mutum

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun kara tabbatar da yaɗuwar cutar zuwa karamar hukumar Zurmi da kuma karamar hukumar Isa a jihar Sokoto.

Garin Zamfara da aka fara samun cutar

Cutar dai an fara samunta ne a kauyen Tsibiri da ke karamar hukumar Maradun a watan Fabrairu.

An fara samun cutar ne a kauyen Tsibiri da ke karamar hukumar Maradun a watan Fabrairu.

Rahotanni da suka fito daga kauyen Tsibiri sun nuna cewa mutanen da cutar ta kashe daga watan Fabrairu zuwa 12 ga Mayu sun kai hudu.

An kuma samu mutane sama 228 da cutar ta kama a kauyen tare da mika 10 zuwa cibiyar yaki da cututtuka da ke Gusau.

Zamfara: Halin da ake ciki a Shinkafi

A karamar hukumar Shinkafi ma an samu bullar cutar a kauyen Galadi tun cikin watan Afrilu.

Wani ma'aikacin lafiya a asibitin Shinkafi ya tabbatar da mutuwar mutane shida cikin mutum 100 da cutar da kama.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar jihar Niger zai aurar da marayu 100

Kira zuwa ga gwamnatocin Zamfara da Sokoto

Ma'ikacin lafiyar ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Zamfara da Sokoto kan yin haɗaka wajen magance yaɗuwar cutar.

Ya ce akwai bukatar daukan matakan gaggawa a wuraren da aka samu cutar domin gudun shiga wasu yankuna.

Jawabin gwamnatin jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara dai ta tabbatar da bullowar bakuwar cutar tun lokacin da ta fara kama mutane.

Kwamishinar lafiya ta jihar, Dakta Aisha Anka ta ce alamomin cutar sun hada da zazzabi, ciwon ciki kuma tana da alaƙa da shan gurbataccen ruwa.

Ta kuma kara da cewa sun riga sun mika rahotan ga hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya (NCDC).

Yan bindiga sun kashe malami a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyukan manoma a kananan hukumomin Maradun da Tsafe a jihar Zamfara ranar Alhamis da ta wuce.

Rahoto daga yankin ya nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da wani babban malamin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng