Mun turawa yan Najeriya sakonnin wayar da kai 100m kan Korona - NCDC
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, ta ce, ta turawa yan Najeriya sakonnin wayar da kai kan cutar Coronavirus sama da milyan dari (100m) daga watan Febrairu zuwa yanzu.
Hukumar wacce ta bayyana hakan ranar Asabar a shafinta na Tuwita, ta alanta kwanaki 100 da bullar cutar Korona a Najeriya da ta hallaka akalla mutane 300, Dally Nigerian ta gano.
Jawabin yace: "Mun yi hakan ne ta shafukan soshiyal midiya, kafafun yada labarai da wasu sassa na daban domin wayar da kan yan Najeriya kan muhimmancin kare rayukansu da na masoyansu ta hanyar takaita yaduwar COVID-19."
"Sama da sakonni 150 a gidajen rediyo da talabijin na gudana yanzu hakan zuwa dukkan sassan kasar nan."
"Tare da gudunmuwar kamfanonin sadarwan Najeriya, an tura sama da sakonnin waya milyan 100 daga watan Febrairu 2020 domin tunawa yan Najeriya hanyoyin da zasu iya dauka domin kare kansu daga COVID-19."
Hukumar ta kara da cewa tun daga ranar farko, an gwada yan Najeriya 76,802.
Daga cikin wannan adadin da aka gwada, 12,233 ne suka kamu da cutar. Yayinda 3,826 suka samu waraka, 342 sun rasa rayukansu.
KU KARANTA: Yadda aka baiwa matan yan majalisa N80m don zuwa Dubai - Kakakin majalisan Ikko, Obasa
A jiya mun kawo muku rahoton cewa kwamitin diraktocin bankin cigaban Afirika AfDB ta amince da taimakawa Najeriya da bashin $288.5m don takaita illar cutar COVID-19 kan tattalin arziki da al'ummar kasar.
A cewar jawabin da ta saki ranar Juma'a, bankin zata karfafa shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi wajen dakile cutar Coronavirus.
Babban diraktar bankin kan Najeriya, Evrima Faal, yace: "Shirin da za'a kaddamar zai tabbatar da cewa an taimaki tattalin arzikin domin iya jure duk irin girgizan da cutar COVID-19 zai haifar."
"Bankin ta kafa hanyoyin sa ido da bibiyan yadda za'a kashe wadannan kudaden na COVID-19 tare da tattaunawa na musamman da ofishin Odito Janar na Najeriya domin tabbatar da cewa an yi gaskiya da ayyuka da kudaden,"
TSOKACI: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng