Wutar Lantarki: ’Yan Kwadago Sun Fusata, Sun Rufe Ofishin Hukumar NERC a Abuja

Wutar Lantarki: ’Yan Kwadago Sun Fusata, Sun Rufe Ofishin Hukumar NERC a Abuja

  • Kamar yadda su ka ba mambobinsu umarni a daren jiya Lahadi, kungiyoyin kwadago sun rufe hedikwatar hukumar kula da wutar lantarki
  • Haka zalika, mambobin NLC da TUC sun kuma rufe ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki a fadin kasar a yau Litinin, 13 ga Mayu
  • Wannan zanga-zangar da rufe ofisoshin na zuwa ne yayin da hukumar NERC ta gaza janye karin kudin wutar da ta yi ga 'yan sahun 'Band A'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - 'Ya 'yan kungiyoyin kwadago sun rufe babban ofishin hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) a Abuja saboda karin kudin wutar lantarki.

'yan kwadago sun rufe hedikwatar hukumar NERC a Abuja
Kungiyoyin kwadago sun rufe ofishin hukumar NERC da na DisCos a fadin Najeriya.
Asali: Facebook

Zanga-zanga saboda karin kudin wuta

Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun kuma rufe ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki a fadin kasar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kungiyar kwadago za ta rufe ofisoshin rarraba hasken lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar kwadagon, a daren jiya Lahadi, ta aika da sanarwar tunatarwa ga dukkanin rassanta, ofisoshi da kuma abokan huldar ta dangane da shirin gudanar da zanga-zangar da za ta fara a fadin kasar a ranar Litinin.

Gidan talabijin na Arise ya ruwaito 'yan kwadagon za su yi zanga-zangar ne saboda karin kudin wutar lantarki da kuma cire tallafin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

An ce 'yan kwadagon za su rufe ofisoshin hukumar NERC, hedikwatar ma’aikatar wutar lantarki da kuma ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki na jihohi.

Lantarki: An rufe ofisoshin NERC da DisCos

Jaridar SaharaReporters ta ruwaito cewa ma’aikatan hukumar NERC a halin yanzu sun yi cirko-cirko a waje yayin da ‘yan kwadago suka hana su shiga ofishin.

Tun da fari, mun ruwaito maku cewa 'yan kwadagon sun rufe ofishoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki na Jos, Lagos da kuma Oyo.

Kara karanta wannan

Karin kudin wutar lantarki: Kungiyar kwadago ta rufe ginin kamfanin DisCos a Jos

Haka zalika, akwai rahotannin da ke cewa mambobin NLC da TUC sun sha alwashin garkame dukkanin ofisoshin rarraba wutar lantarkin, har sai an janye karin kudin wutar da aka yi.

Gidan talabijin na AIT ya wallafa bidiyon yadda 'yan kwadagon suka mamaye ofishin NERC, kalla a kasa:

Wadanda ke shan wuta a karkashin 'Band A'

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa, akalla anguwanni 481 ne ke karkashin rukunin 'Band A' wadanda ke samun wutar lantarki na awanni 20 a rana.

Hakan na nufin cewa, karin kudin da aka yi na wutar daga N66 zuwa N255 a kan kowace kilowatt (kW) ya shafi iya wadannan anguwannin ne ba duka Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel