Gwamna Ya Sanya Tukuici Mai Tsoka Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yan Sanda 2 a Enugu

Gwamna Ya Sanya Tukuici Mai Tsoka Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yan Sanda 2 a Enugu

  • Ƴan bindiga sun kai hari kan jami'an ƴan sanda a jihar Enugu yayin da suke gudanar da aikinsu a wani sabon hari
  • Miyagun ƴan bindigan ɗauke da makamai sun hallaka jami'an ƴan sanda biyu bayan sun kai musu farmaki a wani wajen shingen binciki
  • Gwamna Peter Mbah ya sanya tukuicin N10m kan maharan waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB/ESN ne da suka kashe jami'an tsaron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Wasu ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda biyu a wani hari da suka kai a shingen binciken ababan hawa a jihar Enugu.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan wasu ƴan bindiga sun hallaka ƴan sanda biyu da ƴan sa-kai uku a ƙauyen Igga da ke ƙaramar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da ƴan bindiga a ƙauyuka 2, sun ceto mutane da yawa a Katsina

'Yan bindiga sun hallaka 'yan sanda a Enugu
Gwamna Peter Mbah ya sanya tukuicin N10m kan 'yan bindigan da suka hallaka 'yan sanda a Enugu Hoto: Peter Mbah
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na daren ranar Juma’a, a lokacin da suke gudanar da aikin bincike a kan titin 'Presidential Road' da ke Enugu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sanda

A cewar kakakin rundunar ƴan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ana zargin cewa maharan ƴan ƙungiyar IPOB/ESN ne waɗanda suka kawo harin a cikin motoci ƙirar SUV guda uku.

Daniel Ndukwe ya ce jami’an sun fafata da ƴan bindigan lamarin da ya tilasta miyagun suka tsere ɗauke da raunuka daban-daban na harbin bindiga.

Ya ce ƴan bindigan sun kuma gudu sun bar wata mota ƙirar Lexus RX 300 mai lamba KTU 991 FD.

Gwamna ya sanya tukuici

Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa Gwamna Peter Mbah ya sanya tukuicin Naira miliyan 10 kan makasan, inda ya ce jihar za ta yi amfani da duk abin da za ta iya yi domin gano su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka kwamandan rundunar NSCDC yayin fafatawa a Benue

Peter Mbah ya yi alƙawarin bayar da wannan tukuicin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar tsaro na jihar a fadar gwamnati da ke Enugu ranar Asabar.

Ƴan bindiga sun hallaka ma'aikacin FIRS

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun farmaki wani matashi a tsakiyar babban birnin tarayya Abuja inda suka yi ajalinsa.

Maharan dai sun biyo matashin wanda ke aiki da hukumar FIRS mai suna Khalid Bichi a Maitama inda suka yi ta harbinsa sai da ya mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng