Sanatan APC Ya Nuna Babban Kuskuren Tinubu Kan Harajin Tsaron Yanar Gizo

Sanatan APC Ya Nuna Babban Kuskuren Tinubu Kan Harajin Tsaron Yanar Gizo

  • Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya caccaki harajin tsaro na intanet inda ya yi nuni da cewa zai talauta ƴan Najeriya sakamakon halin ƙuncin da ƙasar ke ciki a halin yanzu
  • A cewar Ali Ndume, gwamnatin Bola Tinubu na ci gaba da ƙara wa ƴan Najeriya wahala alhalin ba a samar da hanyoyin da za su samu ƙarin kuɗaɗen shiga ba
  • A halin da ake ciki, babban bankin Najeriya (CBN), ta hanyar takardar da ya fitar ya bayyana cewa za a fara aiwatar da harajin nan da makonni biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai tsawatarwa a majalisar dattawa Sanata Ali Ndume, ya yi Allah-wadai da sabon harajin da babban bankin Najeriya (CBN) ya ɓullo da shi.

Kara karanta wannan

"Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 135, ceto mutum 140 da aka sace", DHQ

Bankin na CBN dai ya umurci bankunan ajiyar kuɗi a ƙasar nan da su fara cire kaso 0.5% na harajin tsaro ta yanar gizo a ranar Litinin 6 ga watan Mayu.

Ndume ya caccaki sabon harajin CBN
Sanata Ali Ndume ya ce ba daidai ba ne kara nauyin haraji kan mutane Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sen. Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan ranar 6 ga watan Mayu, 2024, wacce CBN ya aika ga bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane kuskure gwamnatin Tinubu ta yi?

Sai dai, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, ba daidai ba ne gwamnatin tarayya ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ci gaba da tatse ƴan Najeriya ba tare da yin wani abu da zai ƙara musu kuɗin shiga ba.

Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Juma'a, 10 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Bakuwar cuta ta bulla a Zamfara, an rasa rayukan bayin Allah

Sanatan ya ce shirin sanya harajin da ake yi ta yanar gizo zai ƙara yawan harajin da ƴan Najeriya suke biya.

"Ba daidai ba ne a yi ta ƙaƙaba haraji kan mutane yayin da ba ƙara musu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga aka yi ba. Hanyoyin samu kuɗaɗen shiga ba su ƙaru ba, ba ku faɗaɗa su ba. Ba na cikin masu goyon bayan a yi ta tatsar mutane ba gaira ba dalili."

- Sanata Ali Ndume

CBN ya haƙura da karɓar haraji

A wani labarin kuma, kun ji cewa Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan kasuwanci su dakatar da karbar la'adar ajiya har sai zuwa watan Satumba.

Bankin ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Adetona Adedeji, daraktan sa ido kan harkokin bankuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng