"Zamu Ceto Su," Gwamna Ododo Ya Mayar da Martani Kan Sace Daliban Jami'a a Kogi
- Gwamna Ahmed Ododo ya tabbatar wa iyaye da al'ummar jihar Kogi cewa za a ceto ɗaliban jami'a da aka sace cikin ƙoshin lafiya
- Ododo ya bayyana cewa yanzu haka jami'an tsaro da ɗaruruwan mafarauta da suka san yankin sun bazama domin ceto ɗaliban
- Tun farko wasu ƴan bindiga sun shiga jami'ar kimiyya da fasaha ta CUSTEC, inda suka tafi da ɗalibai masu shirin fara jarabawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Gwamna Ahmed Usman Ododo ya kwantar da hankulan iyayen ɗaliban jami'ar kimiyya da fasaha (CUSTEC), Osara, waɗanda aka yi garkuwa da su.
Gwamna Ododo ya tabbatar wa ɗaukacin mazauna Kogi cewa za a ceto ɗaliban jami'ar cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce tuni aka tura ɗaruruwan jami'an tsaro tare da mafarautan da suka san lungu da saƙo a yankin domin ceto waɗanda ƴan bindigar suka sace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar ranar Jumu'a.
Yadda aka sace ɗaliban CUSTEC a Kogi
Idan ba ku manta ba mun kawo maku rahoton cewa wasu ƴan bindiga sun shiga jami'ar (CUSTEC) da ke Osara, sun yi garkuwa da wasu daga cikin ɗalibai.
Wani ganau ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun far wa jami’ar da misalin karfe 9:00 na dare yayin da daliban ke karatun jarabawar da za su yi.
Gwamna Ododo ya mayar da martani
Da yake mayar da martani kan lamarin da safiyar yau Jumu'a, gwamnan ya ce ya samu rahoton abin da ya faru kuma ya yi matukar tayar masa da hankali.
Sanarwan ta ce:
"Nan take bayan samun rahoton, gwamnan jihar Kogi, Mai Girma Ahmed Usman Ododo ya tashi tawagar tsaro don bin diddigin maharan tare da tabbatar da ceto daliban da cafke ƴan bindigar.
"Daruruwan mafarautan yankin da suka san lungu da saƙon wurin da kuma jami'an tsaro sun kewaye yankin domin tabbatar da ceto daliban da aka sace a aji. Zuwa yanzu ɗalibai 9 ne suka ɓata.
"Muna kara tabbatar wa dalibai da iyaye da daukacin al’ummar jihar Kogi cewa gwamnati na kan gaba kuma za a ceto dukkan daliban da aka sace a raye."
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya kuma ba da umarnin a sanya jami’an tsaro a kewayen dukkanin manyan makarantun jihar, Vanguard ta ruwaito.
Ƴan sanda sun daƙile hare-hare a Katsina
A wani rahoton jami'an ƴan sanda sun daƙile yunƙurin ƴan bindiga na yin garkuwa da mutane tare da kubutar da wasu bayin Allah a jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ya ce an samu wannan nasara ne a kauyukan Gidan Maga da Unguwar Boka.
Asali: Legit.ng