Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Jihar Jigawa Ya Rasu
- Allah SWT ya yi wa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Garki da Babura, Isa Dogonyaro, daga jihar Jigawa rasuwa
- Marigayin ya rasu ne da safiyar yau Jumu'ah, 10 ga watan Mayu a birnin tarayya Abuja bayan fama da gajeruwar jinya da ya yi
- Yar uwar marigayin Amina Dogonyaro ta tabbatar da rasuwar tare da karin haske kan lamarin da ya shafi sallar da za a yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Rahotanni da ke fitowa sun nuna cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Garki da Babura a jihar Jigawa, Isa Dogonyaro ya rasu.
Yaushe Isa Dogonyaro ya rasu?
Dan majalisar ya rasu ne a yau Jumu'ah, 10 ga watan Mayu a Abuja bayan gajeruwar jinya da ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yar uwar sa mai suna Amina Dogonyaro ta sanar da rasuwar a safiyar yau a shafinta na Facebook tare da bayyana cewa za a masa sallah a masallacin kasa da ke Abuja bayan sallar Juma'a.
Haka zalika abokin aikinsa a majalisar, Bello El-Rufai ya wallafa labarin mutuwar ta shi a safiyar yau Jumu'ah.
Me majalisa ta ce a kan mutuwar?
A yayin da jaridar Daily Trust ta tuntubi mataimakin kakakin majalisar, Philip Agbese, ya tabbatar da cewa shi ma haka ya ga labarin a kafafen sada zumunta.
Philip Agbese ya kara da cewa a yanzu haka suna jiran sanarwa ne daga iyalansa domin tabbatar da rasuwar.
Wane yankin Jigawa yake wakilta a majalisa?
Dan majalisar yana wakiltar mazabun Garki da Babura ne a karkashin jam'iyyar APC mai mulki bayan nasara da ya samu a babban zaben 2023.
Duk da cewa ba shi bane ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar amma daga baya kotu ta bashi nasara bayan ya shigar da kara.
Majalisa ta nemi karin jami'an tsaro a Niger
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta fara duba yiwuwar neman kafa jami'an tsaro na musamman a jihar Niger saboda yawaitar ayyukan ta'addanci.
Rahotanni sun nuna cewa dan majalisa, Isma'ila Musa Modibbo ne ya kawo kudurin tare da ayyana yankunan da suka fi bukatar samun jami'an cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng