'Yan Sanda Sun Yi Artabu da Ƴan Bindiga a Kauyuka 2, Sun Ceto Mutane da Yawa a Katsina

'Yan Sanda Sun Yi Artabu da Ƴan Bindiga a Kauyuka 2, Sun Ceto Mutane da Yawa a Katsina

  • Jami'an ƴan sanda sun daƙile yunƙurin ƴan bindiga na yin garkuwa da mutane tare da kubutar da mutane 13 a jihar Katsina
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ya ce an samu wannan nasara ne a kauyukan Gidan Maga da Unguwar Boka
  • Kwamishinan ƴan sanda ya yabawa jami'an kana ya jaddada cewa ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen tsare al'umma da dukiyoyin su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane da satar shanu a kauyen Gidan-Maga da ke karamar hukumar Malumfashi.

Ƴan sandan sun samu wannan nasara ne bayan wani kiran gaggawa da aka masu cewa ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai farmaki kauyen.

Kara karanta wannan

Plateau: Ƴan bindiga sun kashe bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna a Arewa

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun samu nasara kan ƴan bindiga a hare-hare biyu a Katsina Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan sanda suka ceto mutum 10

Ya ce ƴan sandan da ke hedkwatar Malumfashi sun samu bayanin cewa ƴan bindiga ɗauke da bindigun AK47 sun sace mutum 10 da shanu 16 a ƙauyen.

Bayan haka ne DPO ya tattara jami'an ƴan sanda suka kai ɗauki, inda suka yi musayar wuta da ƴan bindigar.

Sadiq ya bayyana cewa gwarazan dakarun sun samu nasarar daƙile harin tare da ceto mutanen da maharan suka sace da dukkan shanun da suka ɗauka.

A cewar kakakin ƴan sandan, maharan sun tsere daga wurin artabu da jami'an tsaro ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Kwamishinan ƴan sandan Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa,ya yabawa tawagar dakarun ƴan sandan bisa nasarar da suka samu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka kwamandan rundunar NSCDC yayin fafatawa a Benue

Ya kuma jaddada kudirin rundunar ƴan sanda na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Katsina, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ƴan sanda sun ceto matafiya 3

Haka nan a wani ɓangaren, dakarun ƴan sanda sun daƙile harin garkuwa da mutane a kauyen Unguwar Boka da ke gefen titin Funtua zuwa Gusau a yankin Faskari.

Ƴan sandan sun ceto mutum uku da ƴan bindigar suka yi yunkurin sacewa daga wata motar Golf da ta taso daga ƙauyen Yan Kara.

SP Sadiq ya ce:

"'Yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga. A yanzu haka yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike da nufin zakulo wadanda ake zargi da hannu a harin."

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Plateau

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun kai hari kauyen Kayarda, sun kashe mutum huɗu kuma sun jikkata wasu da dama a jihar Filato.

Magajin garin ya bayyana cewa tun bayan harin mutanen garinɓsuka shiga fargaba da zullumi saboda lamarin ya gigita su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262