ICPC: Kotu ta Daure Jami'in Tsaron NSCDC Na Tsawon Shekaru 5 a Kurkuku

ICPC: Kotu ta Daure Jami'in Tsaron NSCDC Na Tsawon Shekaru 5 a Kurkuku

  • Hukuma mai yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta jawo an daure wani kwamandan NSCDC bisa laifin zamba cikin aminci
  • Kwamandan mai suna Christopher Oluchukwu ya karbi makudan kudade a wurin mutane da dama da sunan sama musu aiki
  • Lauyan hukumar ICPC, Ibrahim Garba ya bayyana yadda ayyukan zamba da Christopher ya yi suka sabawa dokar kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta kama kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC, Christopher Oluchukwu bisa zamba.

ICPC vs NSCDC
Kotu ta daure kwamnadan NSCDC bisa laifin zamba. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Laifin da kwamnadan NSCDC ya aikata

An samu Kwamandan da laifi ne bayan an gurfanar da shi a gaban babbar kotun jihar Katsina bisa karban makudan kudade a wurin wasu mutane uku.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ba masu sana'ar PoS wa'adin watanni 2 su yi rijista da hukumar CAC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ICPC ta bayyana a shafin ta na Facebook cewa mista Christopher ya karbi kudade a wurin mutanen ne da sunan nema wa 'ya'yansu aikin NSCDC.

ICPC: Kudin da jami'in NSCDC ya karba

An ruwato cewa an kama shi da laifin karban kudade daban-daban wadanda suka hada da N200,000, N300,000 da kuma N400,000 a wurin mutanen.

Mutanen sun yi karar kwamandan ne ga hukumar ICPC bayan ya gagara samarwa 'ya'yansu aikin kuma ya ki dawo musu da kuɗinsu.

A yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, lauyan ICPC ya bayyana yadda kwamandan ya sabawa sashe na 8, 10 da 19 na dokar cin hanci da rashawa na shekarar 2000.

Kotu ta daure ma'aikatan banki

A wani rahoton kuma, kun ji cewa kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar ga wasu ma'aikatan bankin Keystone guda biyu da wani mutum dan Indiya.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da ake zargi da safarar makamai ga 'yan bindiga a Kano

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta samu mutanen da aikata laifuffuka har 7 da suka shafi satar N855m da kuma zamba cikin aminci ga abokan huldar bankin da suke aiki.

Kasancwar sun daukaka kara ne, sabon hukuncin da kotun ta yi ya zama tabbaci ne kan hukuncin da babbar kotun Legas ta fara yanke wa mutanen tun a shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng