Zamba cikin aminci: 'Yan sanda sun garkame wata matar aure
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gurfanar da wata matar aure mai shekaru 27, Ngozi Mbionwu a gaban Area Court Grade I na babban birnin tarayya Abuja bisa zarginta da cin damfara.
'Yan sandan sun gurfanar da ita bisa aikata laifuka biyu masu alaka da cin amana da zamba cikin aminci.
Mai shigar da karar, Mr Babajide Olanipekun ya shaidawa wata Chidinma Lawrence ce ta shigar da kara a ofishin 'yan sanda da ke Kubuwa a ranar 7 ga watan Fabrairun 2019.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun yanka ma su sana'ar gawayi 18 a Borno
Ya ce wanda ake tuhumar ta damfari diyar wanda ta shigar da karar mai shekaru 13 inda ta sanya ta bata kayan abinci wadda kudinsa ya kai N81,000.
Ya ce laifin ya sabawa sashi na 311 da 322 na dokar Penal code.
Wadda ake tuhumar ta musanta aikata laifukan.
Alkalin kotun, Ibrahim Balarabe ya bayar da belin wanda ake tuhumar a kan kudi N80,000 tare da mutum daya da zai karbe ta beli wanda kuma dole ya kasance yana zaune kusa da kotun.
Ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Maris kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng