An Ƙara Yi Wa Dakarun Sojoji Sama da 20 Kisan Gilla a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

An Ƙara Yi Wa Dakarun Sojoji Sama da 20 Kisan Gilla a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton da ake yaɗawa cewa an yi wa sojoji 21 kisan gilla a Onitsha ta jihar Anambra
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya yi kira ga ɗaukacin al'umma su yi watsi da ƙagaggen labarin
  • Haka nan kuma rundunar sojojin Najeriya ta zargi haramtacciyar ƙungiyar ƴan a-ware IPOB da yaɗa wannan ƙarya domin ta ja hankalin mutane

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton da ke yawo cewa an kashe dakarun sojoji 21 a Onitsha da ke jihar Anambra.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ne ya ƙaryata rahoton a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 8 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka kwamandan rundunar NSCDC yayin fafatawa a Benue

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton yi wa sojoji 21 kisan gilla a jihar Anambra Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

'Yan sanda: "Ba a kashe sojoji ba"

'Dan sandan roƙi ɗaukacin ƴan Najeriya su yi watsi da labarin wanda ya bayyana a matsayin ƙarya, kamar yadda Tribune Nigeria ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, babu wani abu mai kama da kisan sojoji da ya faru ranar Litinin da yamma kamar yadda ake yaɗawa.

IPOB ta yaɗa labarin kisan sojoji?

Jami'an tsaro sun ɗora laifin yaɗa wannan jita-jita a wuyan ƙungiyar ƴan ware (IPOB), inda suka ce shugabanni da magoya bayan kungiyar na neman jan hankali ne kawai.

Jaridar Punch ta ruwaito Ikenga na cewa:

“Rundunar ‘yan sandan Anambra tana sane da wani rahoto na yaudara, mara tushe, kuma na karya mai taken, ‘Yan bindiga sun kashe sojoji 21 a Anambra’, wanda wasu kafafen yada labarai na intanet da jaridu suka watsa.
"Muna tabbatar da cewa wannan rahoton ba gakiya ba ne, kirkirarren abu ne da wasu ɓata gari suka kirkiro."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan canji 17 a kasuwar musayar kuɗi a jihar Kano

Rundunar sojoji ta yi martani

A nasa ɓangaren, kakakin rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya, Majo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce labaran karya na daga cikin farfagandar da IPOB ke amfani da su a matsayin dabarunta.

Daily Trust ta rahoto Nwachukwu na cewa:

“Na tuntubi hedikwatar runduna ta 82, wanda jihar Anambra ke ƙarƙashinta, kuma bayanan da suka zo min na cewa labarin karya ne. Farfaganda ce ta IPOB/ ESN."

Ƴan bindiga sun kai hari a Benue

A wani rahoton kun ji cewa ƴan bindiga da ba a sani ba sun kai hari makarantar sakandire a kauyen Adeke da ke jihar Benuwai ranar Talata da daddare

Daraktan yaɗa labarai na cocin katolika a Makurɗi ya tabbatar da kai harin amma ya ce babu abin da ya samu shugaba da ɗaliban makarantar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262