Sojoji Sun Dauki Mataki Bayan Kwashe Kwanaki a Kauyen da Aka Kashe Jami'ai

Sojoji Sun Dauki Mataki Bayan Kwashe Kwanaki a Kauyen da Aka Kashe Jami'ai

  • Daga ƙarshe rundunar sojojin Najeriya ta janye dakarunta daga ƙauyen Okuama na ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta
  • Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar ne ya tabbatar da janyewar sojojin daga ƙauyen a ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2024 bayan sun kwashe kwanaki a cikinsa
  • Sojojin sun mamaye ƙauyen ne biyo bayan kisan gillar da aka yi wa jami'an tsaro 17 da suka je aikin kwantar da tarzoma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Dakarun sojojin Najeriya sun janye daga ƙauyen Okuama na ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Gwamnan jihar, Sheriff Oborevwori ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024.

Sojojin sun janye daga Okuama
Sojoji sun janye daga kauyen Okuama na jihar Delta Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a gidan gwamnatin jihardake Asaba, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna ya ɗauki zafi yayin da APC ta umurci majalisa ta tsige shi nan take

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwmanan ya bayyana cewa mutanen Okuama da suka rasa matsugunansu yanzu sun samu damar komawa gidajensu.

Ya kuma bayyana cewa sansanin ƴan gudun hijira (IDP) da gwamnatinsa ta kafa domin tsugunar da mazauna Okuama da suka rasa matsugunnansu yana ci gaba da aiki.

Bisa ga wannan sanarwar da gwamnan ya fitar, ana sa san mutane za su koma gidajensu domin sake gina abin da ya yi saura.

Meyasa sojoji suka mamaye Okuama?

Sojoji sun mamaye ƙauyen ne bayan kashe jami’an sojoji 17 da ƴan ta'adda suka yi a ranar 14 ga watan Maris, 2024 a yankin da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Mamayar sojojin ta sanya mazauna yankin da dama suka tsere zuwa sauran garuruwan da ke makwabta da su.

Sojojin guda 17 da suka haɗa da kwamandan bataliya ta 181, manjo guda biyu, kyaftin ɗaya da sojoji 12 na bataliyar an binne su a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

Ƴan ta'adda sun hallaka sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa Aƙalla sojoji 17 ne wasu ƴan ta'adda a ƙauyen Okuoma suka halaka a ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Sojojin na Bataliya ta 181, Bomadi, sun je aikin ceto ne a lokacin da maharan suka yi musu kwanton ɓauna a ranar Alhamis 14 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng