Dubu Ta Cika: An Kama 'Yan Canji 17 a Kasuwar Musayar Kuɗi a Jihar Kano
- Ƴan sanda da haɗin guiwar jami'an DSS sun damƙe ƴan canjin da suka yi haye a kasuwar musayar kuɗi Wapa da ke jihar Kano
- Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya ce jami'an sun kama waɗanda ake zargi 29 amma daga bisani aka wanke 12 daga ciki
- Ya shawarci ɗaiɗaikun mutane da ƴan kasuwar hada-hadar kuɗi su tabbata sun bi tsarin doka kuma sun mallaki lasisi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Dakarun ƴan sanda sun kama wasu mutum 17 bisa zargin sun yi wa kasuwancin musayar kuɗi haye a jihar Kano.
Jami'an rundunar ƴan sandan sun samu nasarar kama waɗanda ake zargin ne a kasuwar Wapa da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar ta Arewa maso Yamma.
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Usaini Gumel ne ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta Najeriya (NAN) a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ruwaito kwamishinan na cewa:
"Jami'an ƴan sanda ne suka jagoranci kai samame a kasuwar hada-hadar kuɗi ta Wapa da ke ƙaramar hukumar Fagge tare da jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS).
"Jimulla mun kama mutum 29 wanda daga cikinsu kuma an wanke mutum 12 daga zargi. Mun kwato CFA 68,000, da Rufi 30 (Kudin Indiya) daga hannun su.
"Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa kuma za a gurfanar da su a gaban kotu."
CP Gumel ya yabawa jami'an tsaro
Kwamishinan ƴan sandan ya yabawa rundunar hadin guiwa bisa jajircewa da hadin kai wajen ganin an samu nasarar wannan aikin, rahoton Tribune.
"Matakan da aka ɗauka sun nuna ƙarara cewa ba zamu amince da duk wata hada-hadar kuɗi ba bisa ƙa'ida ba kuma duk wanda aka kama da laifin zai fuskanci fushin doka," in ji shi.
Ya shawarci mutane da ’yan kasuwa a bangaren hada-hadar kudi da su rika gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka, su nemi lasisi kuma su kaucewa ayyukan da suka saɓa doka.
EFCC ta kama ƴan canji a Abuja
A wani rahoton Jami'an hukumar EFCC sun waiwayi ƴan canji, sun cafke wasu a kasuwar bayan fage da ke Wuse 4 a birnin tarayya Abuja ranar Talata.
Wannan mataki da EFCC ke ɗauka na zuwa ne biyo bayan matakan da gwamnatin tarayya da babban banki CBN ke ɗauka na farfaɗo da darajar kuɗin Najeriya.
Asali: Legit.ng