Sarkin Musulmi Ya Buƙaci Musulman Najeriya Su Fara Duba Jinjirin Watan Zhul-Qa'ada

Sarkin Musulmi Ya Buƙaci Musulman Najeriya Su Fara Duba Jinjirin Watan Zhul-Qa'ada

  • Sarkin Musulmi ya buƙaci a fara duba jinjirin watan Zhul-Qa'ada ranar Laraba, 29 ga watan Shawwal watau 8 ga watan Mayu, 2024
  • A wata sanarwa da fadar Sarkin ta fitar a Sakkwato, Sultan ya roki musulmi su kai rahoton ganin watan ga dagaci ko hakimi mafi kusa da su
  • Zhul-Qa'ada shi ne watan 11 a cikin jerin watannin Addinin Musulunci kuma daga shi sai watan babbar Sallah watau Sallar layya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar musulmi su fara duba jaririn watan Zhul-Qa'ada.

Sarkin musulmin ya buƙaci a fara duban jinjirin watan daga yau Laraba, 29 ga watan Shawwal, 1445/AH wanda ya zo daidai da 8 ga watan Mayu, 2024.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisa ya nemi afuwa bayan 'yan majalisu sun kusa ba hammata iska

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.
Sultan ya roƙi ɗaukacin al'ummat Musulmin Najeriya su fara duba jinjirin watan Zhul-Qa'ada Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin Musulunci na masarautar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar a Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a tura saƙo ga Sultan

Sultan ya buƙaci duk wanda Allah ya nuna masa jinjirin watan ya kai rahoto ga hakimin yankinsa domin isar da saƙon ga Sarkin Musulmi, jaridar Vanguard ta tattaro.

Sanarwan ta ce:

"Muna sanar da al'ummar Musulmi cewa ranar Laraba, 8 ga watan Mayu daidai da 29 ga watan Shawwal, 1445AH, ita ce ranar da ya kamata a duba jinjirin watan Zhul-Qa'ada, 1445AH.
"Bisa haka muna rokon Musulmi su duba jinjirin watan yau Laraba kuma su miƙa rahoton ganin watan ga dagaci ko hakimi domin isar da saƙon ga Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar CFR."

Idan baku manta ba Sarkin Musulmi shi ne shugaban majalisar ƙoli ta harkokin shari'ar Musulunci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana lokacin dawowar Tinubu gida Najeriya

Watan Zhul-Qa'ada shi ne wata na 11 a cikin jerin watannin Musulunci kuma daga shi sai watam Zhul-Hijjah wanda Musulmi ke gudanar da sallar layya.

NNPC zai kawo ƙarshen wahalar Fetur

A wani labarin na daban Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPLC) ya dauki sabon mataki domin kawo karshen dogayen layuka a gidajen mai

Jami'in yada labaran kamfanin, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa ya kamata 'yan Najeriya su daina tada hankali domin matsalar man fetur ta zo karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262