CBN Ya Hakura, Ya Fasa Karbar Kudaden da Ya Yi Niyya Wajen Ajiya a Banki

CBN Ya Hakura, Ya Fasa Karbar Kudaden da Ya Yi Niyya Wajen Ajiya a Banki

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da karɓar la'adar ajiya daga wajen masu ajiyar kuɗaɗe a bankunan kasuwancin ƙasar nan
  • CBN a cikin wata sanarwa ya umurci bankuna da su dakatar da karɓar kuɗaɗen har sai zuwa nan da ƙarshen watan Satumban 2024
  • Batun cirar kuɗaɗen wanda aka dawo da shi a 1 ga watan Mayu ya fusata abokan hulɗa na bankuna waɗanda suka nuna rashin yardar su da hakan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan kasuwanci su dakatar da karbar la'adar ajiya har sai zuwa watan Satumba.

Bankin ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Adetona Adedeji, daraktan sa ido kan harkokin bankuna.

Kara karanta wannan

Jami'an EFCC sun waiwayi ƴan canji yayin da darajar Naira ke ƙara faɗuwa a Najeriya

CBN ya dakatar da tsarin cirar la'ada a kudaden ajiya
CBN ya dakatar da karbar la'ada a kudaden ajiya Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Bankin CBN ya yi amai ya lashe

Hakan ya biyo bayan zanga-zangar da abokan cinikin wasu bankunan ajiya suka yi na nuna adawa da cire kuɗaɗen, wanda aka dawo da shi a ranar 1 ga watan Mayu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi niyyar za a riƙa cirar kaso 2% cikin 100% na kuɗaɗen ajiyar ɗaiɗaikun mutane da suka kai sama da N500,000.

Ana da labari cewa ga masu asusun kamfani za a cire musu kaso 3% cikin 100% na kuɗaɗen ajiya da suka kai sama da N3m.

Sai dai, a cikin sanarwar babban bankin na CBN ya fitar, ya ba da umarnin a dakatar da cirar kuɗin na tsawon watanni uku masu zuwa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Bayanin da CBN ya yi daga baya

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

Abia: Tsohon shugaban majalisa, tsofaffin ciyamomi da ƙusoshi sun fice daga PDP

"Babban bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa'adin dakatar da karɓar la'adar 2% da 3% da ake yi a baya kan kuɗaɗen ajiya har sai zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024."

Babban bankin ya umarci cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su ci gaba da karɓar duk wasu kuɗade daga jama’a ba tare da cirar wani kaso ba har zuwa ƙarshen watan Satumba.

CBN ya ɓullo da sabon haraji

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara karbar harajin kaso 0.5% domin turawa 'asusun tsaron yanar gizo.'

Kuɗaɗen dai za a a riƙa cire su ne da zarar abokan hulɗar bankunan sun tura kudi daga asusunsu ta yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng