"Za mu Dauki Kwararan Matakai kan Barayin Gwamnati", EFCC

"Za mu Dauki Kwararan Matakai kan Barayin Gwamnati", EFCC

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ja kunnen masu yiwa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa domin sun shirya daukar matakan da suka dace
  • Shugaban EFCC, Ola Olukoyede da ya yi barazanar ba za su saurarawa dukkanin wadanda aka kama da laifin illata tattalin arzikin kasar nan ba idan aka kama su da dibar kudin gwamnati
  • Ya bayyana haka ne a taron shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua kan shugabanci da bayar da kyaututtuka karo na farko da Global Initiative for Leadership Success ta shirya a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ja kunnen masu yiwa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.

Kara karanta wannan

Kungiya ta maka gwamnoni 36 da minista Wike a kotu kan cin bashin N5.9tn da $4.6bn

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya yi barazanar ba za su saurarawa dukkanin wadanda aka kama da laifin illata tattalin arzikin kasar nan ba.

Hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta gargadi masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne a taron shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua kan shugabanci da bayar da kyaututtuka karo na farko da Global Initiative for Leadership Success ta shirya a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar EFCC ta ce a tsaye ta ke

Hukumar EFCC ta bayyana cewa a tsaya take cak wajen yakar cin hanci da rashawa a kasar nan.

Ola Olukoyede shugaban hukumar, wanda ya samu wakilcin Daraktan yada labaran hukumar, Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan, kamar yadda withinnigeria ta wallafa.

“ Duk wanda ya saci kudin gwamnati ba zai ci banza ba. Mun fito da niyyar yakar duk wasu laifuffuka da nagarta.”

Kara karanta wannan

Wasu 'yan jam'iyyar APC sun yi kira ga EFCC kan cigaba da binciken ministan Tinubu

Ya ce ba za su saurarawa duk wadansu da aka kama da yin almundahanar kudaden jama'a ba.

EFCC ta musanta tuhumar tsofaffin gwamnoni

Mun ruwaito muku cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta musanta cewa ta fitar da jerin sunayen wasu tsofaffin gwamnoni hamsin da takwas a kasar nan.

Kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya ce labarin cewa ana tuhumar tsofaffin gwamnonin da almundahanar N2.187tn yaudara ne kawai da karya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.