Tsohon Ministan Buhari Ya Faɗi Yadda Wasu Hadimai Suka 'Saci Kuɗi' a Gwamnatin APC

Tsohon Ministan Buhari Ya Faɗi Yadda Wasu Hadimai Suka 'Saci Kuɗi' a Gwamnatin APC

  • Adebayo Shittu ya ce hadiman da ke kewaye da Muhammadu Buhari sun yi amfani da yardarsa sun ci amanar ƙasar nan
  • Tsohon ministan sadarwa ya bayyana cewa an tafka maguɗi da yawa kuma sun amince da abubuwa da ba tare da Buhari ya sani ba
  • Ya kuma roki hukumar EFCC ta gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka haɗa baki da Emefiele ba tare da sanin shugaban ƙasa ba a lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Adebayo Shittu, ya ce an tafka maguɗi da zamba masu ɗumbin yawa a tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe karkashin Muhammadu Buhari.

Shittu ya yi aiki a zangon mulkin Buhari na farko kuma ya bayyana yaƙinin cewa da yawan makusantan Buhari sun yi amfani da damarsu sun talauta ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Jami'an EFCC sun waiwayi ƴan canji yayin da darajar Naira ke ƙara faɗuwa a Najeriya

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Tsohon ministan Buhari ya ce an tafka maguɗi da yawa a gwamnatin da ta gabata Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Ya ce abubuwan da waɗanda suke kewaye da tsohon shugaban ƙaar suka aikata ne suka duƙusar da tattalin arzikin ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake martani kan zargin cewa gwamnatin Buhari ta riƙa buga kuɗi domin tafiyar da harkokin mulki, tsohon ministan ya ce:

"Bari na faɗa muku wani abu, an tafka maguɗi da yawa, na samu labarin cewa an amince da abubuwa da dama waɗanda ko kaɗan Buhari bai sani ba."

Adebayo Shitttu ya bayyana haka ne a cikin shirin Sunrise Daily na Channels TV ranar Talata.

Yadda aka tafka 'sata' a mulkin Buhari

"An tafka magudi da dama da kuma sa hannun damfara wadanda ba daga wajen Shugaban kasa suka fito ba. Ina faɗa muku da gaske abubuwa da dama bai san an yi ba.
"Akwai mutanen da ke kewaye da shugaban ƙasa a lokacin waɗanda suka yi amfani da yardar da ya musu, suka haɗa baki da gwamnan CBN na lokacin."

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

- Adebayo Shittu.

Ikirarin tsohon ministan ya yi daidai da kalaman kakakin shugaban ƙasa Tinubu, Ajuri Ngelale, wanda ya ce galibin umarnin cire kuɗi a CBN karkashin Emefiele ba su ɗauke da sa hannun Buhari.

Shittu ya buƙaci EFCC tayi bincike

Bisa haka Shittu ya buƙaci hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa da ta shiga lamarin kuma ta gudanar da bincike a tsanake.

"Ina fata EFCC za ta binciki yadda wadannan abubuwa suka faru ba tare da shugaban kasa ya sani ba," in ji Shittu.

Shettima ya soke tafiya Amurka

A wani rahoton na dabama, an ji Kashim Shettima ya fasa tafiyar da aka tsara zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kuwanci a Dallas da ke ƙasar Amurka.

Mataimakin shugaban ƙasar ya soke wannan tafiya ne sakamakon wata tangarɗa da jirginsa ya samu, ministan waje zai wakilci Tinubu a taron

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262