Bankin Duniya Ya Kafawa Najeriya Sharadin Dawo da Haraji Kafin Karbo Bashin $750m
- Bankin duniya ya kafa wa gwamnatin Najeriya sharadin dawo da harajin sadarwa domin samun damar karbar lamuni
- Shugaba Bola Tinubu ya fara neman karbar lamunin dala miliyan 750 ne daga bankin cikin watan Maris da ya gabata
- Rahotanni sun bayyana matakin da ake tunanin gwamnatin Najeriya za ta dauka domin samun damar karban lamunin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Rahotanni da ke fitowa sun yi nuni da cewa gwamnatin Najeriya na shirin dawo da harajin da ta dakatar a watannin baya.
Matakin dawo da harajin yana da alaka ne da kudirin karbo bashin dala miliyan 750 da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke shirin yi daga bankin duniya.
Harajin da bankin duniya yake so a Najeriya
Wani rahoto da Nairametrics ta ruwaito ya nuna cewa sharadin yana cikin yarjejeniyar da Najeriya ta yi da bankin a watan Maris da ya gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa a watan Yulin shekarar 2023 ne shugaba Bola Tinubu ya dakatar da harajin sadarwa a Najeriya da kashi 5%.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sharudan sun hada da dawo da harajin sadarwa da harajin da za a rika karba kan musayar kudi ta banki.
Shin Najeriya za ta yarda da sharadin bashin?
Sai dai kuma a bisa dukkan alamu shugaba Bola Tinubu zai amince da dawo da harajin domin samun damar karban lamunin.
Hasashe ya nuna haka ne saboda a halin yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa ana cigaba da tattaunawa kan lamarin tsakanin Najeriya da bankin duniya.
CBN ta bullo da sabon haraji
A wani rahoton, kun ji cewa bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a Najeriya za su fara karbar harajin kaso 0.5% daga kudaden da abokan hulda ke turawa.
Babban bankin Najeriya (CBN) ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin, tare da kakaba tarar kaso 2% ga duk wanda bai biya harajin ba.
A cewar sanarwar, umarnin zai fara aiki nan da makonni biyu kuma za a rika amfani da kudaden ne domin yaki da ta'addanci a yanar gizo.
Asali: Legit.ng