Gwamnati Ta Ba Masu Sana’ar PoS Wa’adin Watanni 2 Su Yi Rijista da Hukumar CAC

Gwamnati Ta Ba Masu Sana’ar PoS Wa’adin Watanni 2 Su Yi Rijista da Hukumar CAC

  • Gwamnati ta ba kamfanonin kamfanonin da ke sarrafa na'urar PoS wa'adin watanni biyu su yi wa abokan huldarsu rijista da hukumar CAC
  • Shugaban hukumar kula da kamfanoni (CAC), Hussaini Ishaq Magaji ya ce yi wa masu sana'ar PoS rijista zai kare kasuwancinsu
  • A baya dai hukumar sasanta tsakanin bankunan Najeriya ta ce akwai sama da na'urorin PoS miliyan 1.9 da ke hannun abokan hulda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da kamfanoni ta bayar da wa’adin watanni biyu ga kamfanonin da ke sarrafa na'urar PoS.

Gwamnati ta umar masu sana'ar PoS su yi rijista da hukumar CAC
CAC ta ba masu sana'ar PoS miliyan 1.9 wa'adin wata 2 su yi rijista da hukumar. Hoto: Boonchai Wedmakawand
Asali: UGC

PoS sai da rajista a hukumar CAC

Hukumar ta bukaci kamfanonin da su yi wa wakilansu da ‘yan kasuwa da kuma daidaikun mutanen da ke sana'ar PoS rajista da CAC kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da ake zargi da safarar makamai ga 'yan bindiga a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an cimma wannan matsaya ne a ranar Litinin yayin ganawa tsakanin kamfanonin hada-hadar kudi na intanet da shugaban hukumar ta CAC, Hussaini Ishaq Magaji, a Abuja.

Mutane miliyan 1.9 ke sana'a da PoS

A cewar hukumar sasanta tsakanin bankunan Najeriya, akwai sama da na'urorin PoS miliyan 1.9 da ke hannun 'yan kasuwa da wasu daidaikun mutane a fadin kasar.

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban na CAC ya ce matakin na da nufin kare kasuwancin abokan huldar kamfanonin da kuma karfafa tattalin arziki.

Ya kuma jaddada cewa matakin ya samu goyon bayan sashe na 863, karamin sashe na 1 na dokar kamfanoni, CAMA 2020 da kuma ka’idojin CBN na 2013 kan harkokin banki.

Ayyukan zamba da PoS a 2023

Shugaban na CAC ya ce babu bita da kulli ga wasu kungiyoyi ko daidaikun mutane a wa’adin rajistar da aka diba wanda zai kare a ranar 7 ga Yuli, 2024, rahoton jaridar SaharaReporters.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga 'yan fashi a jihar Ekiti

Wannan sabon umarnin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun yawaitar zamba da ya shafi na'urorin PoS da kuma shirin dakatar da cinikin cryptocurrency da CBN ke yi.

Kashi 26.37 na almundahana da aka yi a shekarar 2023 an yi ne ta hanyar na'urorin PoS, a cewar wani rahoto na hukumar sasanta tsakanin bankunan Najeriya.

Bankuna za su caji abokan hulda 0.5%

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna da fara cajar abokan huldarsu 0.5% a dukkanin kudaden da za su tura ta intanet.

A cewar bankin CBN, za a rika tattara wadannan kudaden tare da aika su ka asusun yaki da kutsen yanar gizo na Najeriya, kuma za a kira kudin da suna 'kudin tsaron yanar gizo.'

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.