Mutane Sun Gudu Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kai Hare Hare a Garuruwa 10 a Kaduna

Mutane Sun Gudu Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kai Hare Hare a Garuruwa 10 a Kaduna

  • Yan bindiga sun tarwatsa mazauna kauyuka 10 musamman mata da ƙananan yara a yankin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
  • An tattaro cewa galibin mazauna kauyukan sun zama ƴan gudun hijira a garin Giwa saboda yawaitar hare-haren ta'addanci a yankunansu
  • Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ta fara ɗaukar matakan shawo kan lamarin da ƙara matakan tsaro a garuruwan da lamarin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Rahotanni sun nuna cewa mazauna kauyuka 10 a ƙaramar hukumar Giwa sun gudu sun bar gidajensu saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga.

An tattaro cewa mafi akasarin waɗanda lamarin ya shafa musamman mata da ƙananan yara, sun yi doguwar tafiya a ƙafa domin neman mafaka a cikin garin Giwa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani matashi, Abdullahi ya kashe matarsa kan ƙaramin abu

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Hare-haren ƴan bindiga ya tilastawa mutane da yawa barin gidajensu a kauyukan Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

Wakilin mazaɓar Giwa a majalisar dokokin jihar Kaduna, Umar Auwal Bijimi, ya tabbatar da haka ga jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumomi sun ɗauke Sajan Bagobiri

Umar Auwal Bijimi ya ce mutane sun fara gudun hijira daga kauyukansu ne bayan hukumomi sun ɗauke wani jajirtaccen soja mai kwazo, Sajan Usman Hamisu Bagobiri.

A cewarsa, wannan soja na taka muhimmuyar rawa wajen yaƙar ƴan bindigar da suka addabi yankin, amma kwatsam aka canza masa wurin aiki.

Ya ce tafiyar Sajan Bagobori ya ƙarawa ƴan ta'addan kwarin guiwa, inda suka ci gaba da kai munanan hare-haren ta'addanci, wanda ya tilastawa mutane yin gudun hijira.

Bijimi ya ce kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Gogi, Angwar Bako, Marge, Tunburku, Bataro, Kayawa da Yuna, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin soji da su mayar da Sajan Bagobiri bakin aiki tare da tura karin sojoji jajirtattu domin ci gaba da yaki da ‘yan bindigar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka babban basarake a wani hari cikin gidansa

Wani mazaunin yankin, Korau Fatika ya tabbatar da kalaman Bijimi, yana mai cewa yawaitar hare-hare ya jefa tsoro a zuƙatan mutane, wanda ya sa suka gudu tare da iyalansu.

Hakimin Fatika, Nuhu Lawal Umar, ya buƙaci hukumomi su gaggauta samar da tsaro a yankin kuma ya jaddada buƙatar gwamnati ta kawo ma talakawanta ɗauki.

Wane mataki gwamnatin Kaduna ta ɗauka?

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce tuni suka zauna da masu ruwa da tsaki ciki har da shugaban ƙaramar hukumar Giwa kan lamarin.

Ya tabbatar da cewa lamarin ya isa ga hukumomin da suka dace, kuma an fara aiki tare domin inganta tattara bayanan sirri da kuma karfafa matakan tsaro a ƙauyukan da abin ya shafa.

Ƴan bindiga sun kai hari Kaduna

A wani rahoton na daban kun ji cewa akalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu takwas suka samu raunuka a wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna.

Daniel Amos, 'dan majalisa wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai ta ƙasa, ya ce an kai harin ne a kauyen Ambe da ke ƙaramar hukumar Sanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262