Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Wani Artabu a Jihar Benue
- Ƴan ta'adda sun kwashi kashinsu a hannu bayan sun yi arangama da dakarun sojojin Najeriya masu samar da tsaro a jihar Benue
- Dakarun sojojin sun daƙile yunƙurin yin garkuwa da wasu mutane da ƴan ta'addan suka yi bayan sun yi musu ruwan wuta
- Jami'an tsaron sun kuma ƙwato tarin makamai a hannun miyagun lokacin da suka dira a maɓoyarsu da suke fakewa suna aikata ta'asa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Dakarun sojojin Najeriya sun daƙile wani yunƙurin ƴan ta'adda na yin garkuwa da mutane a jihar Benue.
Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun ceto wasu mutum biyu da aka so a sace a jihar.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa a shafinta na manhajar X (wacce a baya aka fi sani da Twitter).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka kori ƴan ta'adda
Sanarwar ta ce sojojin bayan sun amsa kiran gaggawa, sun kai farmaki a maɓuyar ƴan ta'addan a ƙauyen Tsede da ke kan titin Tor Donga Takum a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.
Ƴan ta’addan sun ranta ana kare bayan da sojoji suka yi musu luguden wuta, lamarin da ya tilasta musu barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Bayan musayar wutan, an kuɓutar mutum biyu da aka yi yunƙurin sacewa masu suna Cif Sano Kursi da Augustine Sada ba tare da wani rauni ba.
Nasarorin da sojoji suka samu a Benue
Sanarwar ta ƙara da cewa tuni aka sada mutanen da aka kuɓutar ɗin da ƴan uwansu.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun ƴan ta’addan sun haɗa da bindiga ƙirar FN guda ɗaya, jigidar bindigar FN guda ɗaya, jigidar bindiga ƙirar AK-47 guda 17.
Sauran sun haɗa harsasai guda 10 na musamman masu kaurin 7.62 mm (Special), harsasai guda 58 masu kaurin mm 7.62 (NATO) da katin ATM 3.
Sojoji sun farmaki ƴan ta'adda a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya na Operation Hadin Kai da Whirl Punch a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya sun kashe ƴan ta’adda masu yawa a hare-haren da suka kai Borno da Neja.
Jiragen yaƙin sojojin sun kuma lalata gine-gine da kayan aikin da ƴan ta'addan suke amfani da su wajen aikata laifuka.
Asali: Legit.ng