Bullar Annoba Ta Sanya an Kulle Makarantu a Jihar Adamawa

Bullar Annoba Ta Sanya an Kulle Makarantu a Jihar Adamawa

  • Gwamnatin jihar Adamawa ta ɗauki matakin makarantu a jihar sakamakon ɓarkewar cutar Kyanda da aka samu a jihar
  • Umurnin rufe makarantun wanda aka fitar a sanar Litinin ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu domin samun damar yin allurar rigakafi
  • Ma'aikatar ilmi ta jihar ta fitar da sanarwar inda ta ƙara da cewa za a sake buɗe makarantun a ranar Litinin, 13 ga watan Mayun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa ta rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu sakamakon ɓarkewar cutar Kyanda a jihar.

Sanarwar rufe makarantun na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi, Aisha Umar, da aka fitar a Yola ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Edo: Shugaban majalisa ya dakatar da ƴan majalisa 3 na PDP da APC, bayanai sun fito

An kulle makarantu a Adamawa
Gwamnatin Adamawa ta rufe makarantu a jihar Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Meyasa aka rufe makarantun Adamawa?

Aisha Umar ta ce an rufe makarantun ne domin daƙile yaduwar cutar da kuma ba hukumar kula da lafiya matakin farko ta jiha (PHCDA) damar yin allurar rigakafi, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin hakan sai ma’aikatar ta sanar da ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2024, a matsayin sabuwar ranar da za a sake buɗe makarantun, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A saboda haka an umurci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su rufe makarantu."

Cutar Kyanda ta hallaka rayuka a Adamawa

Aƙalla yara 42 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar Kyanda a jihar.

Kwamishinan lafiya, Mista Felix Tangwami, ya ce an samu rahoton ɓullar cutar a cikin ƙauyukan da ba su yin allurar rigakafi a jihar.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle: APC ta fadi manufar masu son ganin EFCC ta binciki minista

Felix Tangwami ya bayyana cewa mutum 23 ne suka mutu a ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa sannan mutum 19 sun mutu sakamakon ɓullar cutar a ƙaramar hukumar Gombi ta jihar.

Baƙuwar cuta ta ɓarke a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa kimanin mutum 45 ne suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar wata cuta a ƙauyen Gundutse da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano.

Galibin waɗanda lamarin ya ritsa da su da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi, sun nuna alamun cutar zazzabin cizon sauro, gudawa, da amai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng