Shettima Zai Shilla Ƙasar Waje Duk da Babu Labarin Inda Tinubu Ya Wuce Bayan Taron Saudi
- Kashim Shettima zai kama hanya zuwa ƙasar Amurka domin halartar taron kasuwanci ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, 2024
- Mataimakin shugaban ƙasar zai wakilci Bola Ahmed Tinubu a taron wanda aka shirya gudanarwa a birnin Dallas domin tattauna yadda za a bunƙasa Afirka
- Shettima zai jagoranci wasu tarurruka da nufin bunƙasa harkokin zuba hannun jari a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, zai bar Najeriya zuwa ƙasar Amurka domin halartar taron kasuwanci ranar Litinin, 6 ga watan Mayu.
Shettima zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a taron bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Afirka da nahiyar Afirka na 2024 wanda za a yi a birnin Dallas.
Mataimakin shugaban ƙasar zai bi sahun shugabannin ƙasashen Afirka domin tattauna yadda za a haɗa kan nahiyar domin samar da sakamako mai kyau a harkar kasuwanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai bai shugaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X.
Tinubu da shugabannin Afrika a Amurka
Sanarwar na ɗauke da sa hannun mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha.
Shettima zai bi sahun shugaban ƙasar Liberia, H.E. Joseph Boakai, shugaban Malawi, Lazarus Chakwera, shugaban Angola, H.E. Joao Lourenço da shugaban Botswana, Mokgweetsi E. K. Masisi.
Sauran shugabannin da za su halarci taron sun haɗa da shugaban Cabo Verde, José Maria Neves, da mataimakim firaministan Lesotho Nthomeng Majara.
Abubuwan da Shettima zai yi a taron
Nkwocha ya ce:
"Bayan kammala taron, ana sa ran Shettima zai yi jawabi a taron zuba hannu jari a nahiyar Afirka tare da maida hankali kan amfanin da za a samu.
"Har ila yau, ana tsammanin zai yi jawabi a babban taro kan harkokin noma, wanda zai maida hankali wajen lalubo warakar ƙarancin abinci."
Bayan duk wannan kuma Shettima zai gana da manyan ƴan kasuwa kuma zai jagoranci taron 'zuba hannun jari a Najeriya'.
Wannan na zuwa yayin da har yanzu Bola Tinubu bai dawo Najeriya ba mako ɗaya bayan ya halarci taron tattalin arziki a ƙasar Saudiyya.
"Yar'adua ya miƙa mulki lokacin jinya"
A wani rahoto na daban Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya bayyana yadda aka ɓatar da takardar miƙa mulki da marigayi Umaru Musa Yar'adua ya rubuta lokacin yana jinya.
Ƙanin tsohon shugaban ƙasar ya ce ya shiga damuwa lokacin da mutane suka fara surutu amma da ya bincika sai ya gano inda matsalar take.
Asali: Legit.ng