Attajiri Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Marawa Tinubu baya, Ya Fadi Lokacin Samun Sauyi
- Arthur Eze na ɗaya daga cikin fitattun mutane a Najeriya dake son ganin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu nasara
- Attajirin ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa Tinubu baya, inda ya ce shugaban ƙasa mutum ne na jama’a wanda yake tafiya da kowa da kowa a gwamnatinsa
- Attajirin ɗan kasuwar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci wata coci inda ya ba da gudummawar Naira miliyan 20
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Hamshakin attajirin nan na Najeriya, Prince Arthur Eze, ya bukaci ƴan Najeriya da su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.
Prince Arthur Eze ya kuma yaba da yadda shugaban ƙasan yake tafiya da kowa da kowa a gwamnatinsa ba tare da nuna bambanci ba.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Eze ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon an nuna attajirin yana bayar da gudummawar Naira miliyan 20 ga wata coci.
Me attajirin ya ce a kan Tinubu?
Attajirin ɗan kasuwar ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ba shi da iyaka, cewar rahoton jaridar Nigerian Tribune.
Prince Arthur Eze yayin da yabawa salon mulkin Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ƙasar nan za ta sauya bayan shekara takwas.
Ya kuma yabawa shugaban ƙasar bisa naɗa Dave Umahi a matsayin ministan ayyuka na Najeriya da Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.
"Tinubu ba shi da iyaka. Idan ka je Abuja, za ka ga Wike, ɗan kabilar Ibo a matsayin minista. Umahi ɗan kabilar Igbo ne, a matsayin minista. Babu iyaka. Irin waɗannan muke so."
"Domin haka wannan Najeriya bayan shekara takwas za ta sauya. ta fara canjawa. Yanzu, ina roƙon kowa ya ba shi goyon baya kafin mu mutu.”
- Prince Arthur Eze
Ƴan Arewa da Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar APC Alhaji Iliyasu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na Arewacin Najeriya su marawa Shugaba Bola Tinubu baya.
Musa Kwankwaso ya buƙace su da su yi watsi da ƴan tsirarun da ke sukar gwamnatin shugaban ƙasan a ƙoƙarin da yake na kai ƙasar nan zuwa tudun mun tsira.
Asali: Legit.ng