Gobara Ta Tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau, Tayi Barna
- Wata gobara ta tashi a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau cikin dare a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayun 2024
- Gobarar wacce ta tashi a gidan tsohon Sanatan da ke Mundubawa ta fara ne daga ɗakin girki sannan ta lalata ɗakin matarsa ta uku, Halima Shekarau
- Jami'an hukumar kashe gobara sun yi nasarar kashe gobarar kafin ta yaɗu zuwa sauran wurare a cikin gidan na miliyoyin Naira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - An samu tashin gobara a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a ranar Lahadi da daddare.
Gobarar wacce ta auku a gidan tsohon gwamnan da ke Mundubawa, ta lalata ɗakin matarsa ta uku, Halima Shekarau.
Jaridar Leadership a rahoton da ta fitar ta ce ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba wacce ta fara a ɗakin girkin gidan cikin daren ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ina gobara ta fara a gidan Shekarau?
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, mai ba Shekarau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dakta Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta tashi ne a ɗakin girki na cikin gidan da ke a ƙasan gidan na miliyoyin Naira.
"Muna godiya ga Allah gobarar kawai ta shafi ɗaya daga cikin ɗakunan Malam Ibrahim Shekarau ne kuma tuni jami'an hukumar kashe gobara sun kashe ta."
- Dakta Sule Ya'u Sule
Jaridar Daily Post ta ce kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma bai yi ƙarin bayani ba kan dalilin tashin gobarar.
"Har yanzu muna cikin gidan sannan ka san ba zan iya yin magana a kan komai ba yanzu saboda muna ta ƙoƙarin ganin cewa gobarar ba ta yaɗu ba zuwa sauran wurare ba."
- Saminu Yusuf Abdullahi
Shekarau ya shawarci Tinubu
A wani labarin kuma,.kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan ƴan sandan jihohi.
Shekarau ya shawarci gwamnati kan hana ƴan sandan riƙe makamai bayan tabbatar da su domin daƙile abin da zai je ya dawo.
Asali: Legit.ng