Sojojin Sama Sun Kai Hare-Hare Kan ’Yan Ta’addan Arewa da Barayin Mai a Niger-Delta

Sojojin Sama Sun Kai Hare-Hare Kan ’Yan Ta’addan Arewa da Barayin Mai a Niger-Delta

  • Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta ce ta samu nasarar kakkabe 'yan ta'adda da dama a hare-haren da ta kai Borno da Neja
  • Kakakin rundunar NAF, AVM Edward Gabkwet ya bayyana cewa jiragen yaki sun kashe 'yan ta'adda da lalata makamansu a Chinene
  • A wani harin sama, AVM Gabkwet ya ce rundunar ta kakkabe 'yan ta'adda a Neja, da kuma masu satar danyen mai a Neja Delta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai da Whirl Punch a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya sun kashe ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da suka kai Borno da Neja.

Rundunar sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan 'yan ta'adda a Arewa
Sojojin saman Najeriya sun halaka 'yann ta'adda a jihohin Borno da Neja. Hoto: @NigAirForce
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, AVM Edward Gabkwet, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Yakin Isra'ila kan Hamas: Sojin Isra'ila sun yiwa Falasdinawa 5 kisan gilla a kogin Jordan

Gabkwet ya ce jiragen yakin sojojin da ake amfani da su suna ci gaba da kakkabe 'yan ta'adda, lalata gine-gine da kayan aiki, a cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno

A yankin Arewa maso Gabas ya ce an kai harin ne a ranar 3 ga watan Mayu kuma an kaddamar da shi a kan Chinene, wani yankin da ke cikin tsaunin Mandara.

A cewar kakakin, an kuma lura da motocin bindigu guda bakwai da aka ajiye a karkashin bishiyoyi da ke cikin wannan yankin.

Jaridar The Nation ta ruwaito Gabkwet ya ce jiragen sun yi ruwan bama-bamai a yankunan da kuma lalata motocin bindigun da makamansu.

Sojojin NAF sun kai hari jihar Neja

A cewarsa, rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch ta kai makamancin wannan hari ta sama kan ‘yan ta’addan da ke kai farmaki a kauyen Allawa da ke kusa da garin Shiroro a Neja.

Kara karanta wannan

Yadda ake rijista: Rundunar sojin Najeriya ta sanar da daukar sabbin sojoji a 2024

Kakakin na NAF ya ce an gudanar da farmakin ne biyo bayan sahihan bayanan sirri wanda ya nuna yadda ‘yan ta’adda suka yi hijira zuwa kauyen.

Sojojin NAF sun kai hari Neja Delta

Gabkwet ya kuma ce rundunar ta NAF ta kai hare-hare ta sama a Arewacin Arugbana da Temakiri a yankin Neja Delta, inda aka bude matatun mai ba bisa ka’ida ba.

A cewarsa, ta hanyar wannan farmakin, an rage karfin barayin mai da ke ci gaba da yin zagon kasa da lalata bututun man yankin.

NAF ta kakkabe 'yan ta'adda a Neja

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta yi ruwan bama-bamai a a mabuyar 'yan ta'adda a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

A yayin farmakin, rundunar ta ce ta halaka 'yan ta'addan da dama tare da lalata mabuyarsu bayan wani hari da ake zargin sun kai a yankin da ya yi silar mutuwar sojoji shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.