Zargin N70b: Wasu ’Yan Arewa Sun Goyi Bayan Ministan Tsaro, Bello Matawalle
- Kungiyar masu ruwa da tsaki ta Arewa (NSCF) ta yi martani kan zanga-zangar neman cigaba da binciken ministan tsaro, Bello Matawalle.
- Kungiyar ta yi magana ne ta bakin sakataren ta, kwamared Daniel Yakubu, inda ta ce zanga-zangar bata da wani alaka da cigaban ƙasa
- Ta kuma zargi wasu 'yan siyasa masu yi wa shugaban kasa zagon kasa a Arewa kan zaben sa karo na biyu da ɗaukar nauyin zanga-zangar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A satin da ya wuce ne wani tsagi na jam'iyyar APC suka yi kira ga hukumar EFCC domin cigaba da binciken ministan tsaro, Bello Matawalle, kan karkatar da naira biliyan 70.
Biyo bayan zanga-zangar ne kungiyar masu ruwa da tsaki daga Arewa (NSCF) ta fito tana kare Bello Matawalle daga zargin.
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa kungiyar ta ce masu zanga-zangar neman binciken ministan suna bita da kulli ne ga shugaban kasa Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin sakataren kungiyar NSCF
Sakataren kungiyar kwamared, Daniel Yakubu, ya ce mutanen 'yan adawa ne ga Bello Matawalle bisa ganin ya kara samun karɓuwa a siyasa.
Kwamared Yakubu Ya kara da cewa mutanen suna ganin ministan zai zamo musu barazana ne a siyasance sai suka fito da sabon salon nuna adawa da shi.
Zargin yi wa Tinubu zagon kasa
Kungiyar ta kara tabbatar da cewa wasu ne da suke fargabar rasa mulki cikin 'yan siyasa suka dauki nauyin masu zanga-zangar.
A cewar jaridar Vanguard, kungiyar tana zargin 'yan siyasa da suke so shugaban kasa Bola Tinubu ya rasa kuri'un Arewa ne a zabe mai zuwa suka dauki nauyin zanga-zangar.
An yi kira kan binciken Bello Matawalle
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar APC akida ta yi kira ga hukuma mai yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) kan cigaba da binciken ministan tsaro, Bello Matawalle.
Shugaban kungiyar ne, Malam Musa Mahmud ya fadi hakan bayan zanga-zanga a hedikwatar EFFC da ke Abuja ya kuma bayyana alfanu da Najeriya za ta samu idan EFCC cigaba da binciken.
Asali: Legit.ng