Mahaifiyar Jarumin Dan Sanda Abba Kyari Ta Rasu, an Shirya Jana’izarta a Borno

Mahaifiyar Jarumin Dan Sanda Abba Kyari Ta Rasu, an Shirya Jana’izarta a Borno

  • A safiyar yau Lahadi ne muka samu labarin rasuwar mahaifiyar jajirtaccen dan sandan da aka dakatar, DCP Abba Kyari
  • An ruwaito cewar ta rasu bayan fama da rashin lafiya kuma za a yi jana'izarta a gidansu da ke titin Galtimari, Maiduguri, jihar Borno
  • Har yanzu dai DCP Abba Kyari na fuskantar tuhume-tuhume tun bayan da aka kama shi bisa zargin karbar rashawa da safarar kwayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Borno - Labarin da ya karade kafofin sada zumunta na zamani, musamman a yankin Arewa a safiyar yau Lahadi shine labarin rasuwar mahaifiyar DCP Abba Kyari.

Gidan rediyon Albarka da ke jihar Bauchi, ya sanar a shafinsa na Facebook cewa mahaifiyar jajirtaccen jarumin dan sandan da aka dakatar ta rasu bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

Mahaifiyar DCP Abba Kyari ta kwanta dama
Mahaifiyar jarumin dan sanda Abba Kyari ta kwanta dama, za ayi jana'izarta a Borno. Hoto: Usman Aminu
Asali: Facebook

An shirya yi mata sutura

Shi ma Musa Abdullahi Sufi, wanda ya kasance fitacce a shafin Facebook ya sanar da rasuwar mahaifiyar Kyari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa dattijuwar ta rasu a yau Lahadi, 5 ga watan Mayu, 2025 kuma za a yi mana sutura a gida mai lamba 12, titin Galtimari, Maiduguri, jihar Borno.

Wani masoyin dakataccen jarumin dan sandan, Iliyasu Ibrahim ya sanar da cewa za a yi jana'izar mahaifiyar da misalin karfe 4:00 na yammacin yau lahadi.

Ana ci gaba da tsare Abba Kyari

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin Abba Kyari a kan kudi N50m.

Sai dai kotun ta bayyana cewa ba za a saki dakataccen dan sandan ba duk da wannan beli nasa da aka bayar.

Kara karanta wannan

Tinubu yana amfani da Wike wajen ruguza jam'iyyar PDP? Dele Momodu ya magantu

Kotun ta ce sakin Kyari ya dogara ne ga hukuncin da aka yanke kan tuhumar da ake masa da wasu mutane huɗu kan laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi.

NDLEA ta gurfanar da Abba Kyari

Mun ruwaito maku cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta gurfanar da DCP Kyari da da abokan harkallarsa guda shida a gaban kotu.

Hukumar ta gurfanar da Abba Kyari da mutanen kan tuhume-tuhumen da suka shafi sa hannu a fataucin miyagun kwayoyi zuwa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.