Sanatan NNPP Ya Hango Kuskure a Kasafin Kudin 2024 da Tinubu Ya Sa Hannu

Sanatan NNPP Ya Hango Kuskure a Kasafin Kudin 2024 da Tinubu Ya Sa Hannu

  • Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa ya yi magana kan kasafin kuɗin shekarar 2924 da Shugaba Tinubu ya rattaɓawa hannu
  • Sulaiman Abdurahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa kasafin kuɗin cike yake da kura-kurai waɗanda bai taɓa ganinsu ba
  • Sanatan ya kuma koka kan yadda jam'iyyar APC mai mulki ke tafiyar matsalar tsaro ƙasar nan da ta ƙi ta ƙi cinyewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, ya nuna kura-kurai a cikin kasafin kuɗin 2024, inda ya yi zargin an yi cushe a cikinsa.

Kawu Sumaila, ya bayyana cewa kasafin kuɗin wanda Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓawa hannu cike yake da kura-kurai waɗanda bai taɓa ganin irin su ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shirya daukar mataki mai tsauri kan dan kwangila saboda aikin N6bn

Kawu Sumaila ya magantu kan kasafin kudin 2024
Kawu Sumaila ya hango kura-kurai a kasafin kudin 2024 Hoto: Bola Tinubu, Kawu Sumaila
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa Sanatan ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da wani gidan talabijin na yanar gizo a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ƙudirin kasafin kuɗin bana shi ne kasafin kuɗi mafi kuskure da na taɓa gani.
"A bayyane yake cewa gwamnati ba ta ɗaukar matakan da suka dace domin magance ƙalubalen tattalin arziƙinmu."

Sanata Kawu Sumaila, wanda tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye ne a majalisar wakilai, ya kuma yi magana kan rashin tsaro a ƙasar nan.

Wane kira ya yi ga Tinubu?

Sanatan ya buƙaci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya.

Kawu Sumaila wanda ɗan jam'iyyar NNPP ne ya bayyana matukar takaicinsa da rashin jin daɗinsa kan yadda jam'iyyar APC ke tafiyar da harkokin tsaro a ƙasar nan.

Ya kuma nuna shakku kan yadda hukumomin tsaro za su iya magance matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan yadda ya kamata, inda ya buƙace su da ƙara zagen damtse.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kwara ya halarci kotu yayin da EFCC ta gurfanar da kwamishina kan N1.22bn

Batun cushe a kasafin kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya caccaki Sanata Abdul Ningi kan zargin cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024.

Shugaba Tinubu ya ce duk waɗanda ke zargin yin cushen ya tabbata ba su fahimci ilimin lissafi ba kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng